ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

by Sulaiman
2 months ago
Roƙon Ruwa

Mai Martaba Sarkin Katagum, Dakta Umar Faruk Umar Kabir, ya jagoranci addu’ar roƙon ruwa da aka gudanar a garin Azare, hedikwatar Masarautar Katagum, sakamakon ƙarancin ruwan sama da ake fuskanta a yankin a bana, lamarin da ya haifar da damuwa ga manoma da sauran al’umma.

An gudanar da addu’ar ne a ranar Laraba, 22 ga Yuli, 2026, a Filin Masallacin Idi na Azare da ke kusa da makabartar garin. Dubban al’umma ne suka hallara domin neman taimakon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saukar da ruwan sama mai albarka da zai amfani ƙasa da jama’a.

Taron ya samu halartar manyan malamai, hakimai, masu unguwanni, shugabannin al’umma da ɗimbin jama’a daga Azare da maƙwabtanta. Mahalarta taron sun haɗu cikin tawali’u da ƙanƙan da kai wajen roƙon Allah Ya kawo ƙarshen ƙarancin ruwan saman da ake fuskanta.

ADVERTISEMENT

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kofar Fada da ke Azare, Alaramma Malam Ayuba, shi ne ya jagoranci addu’o’in. Ya roƙi Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya saukar da ruwan sama mai amfani da albarka, ya yalwata amfanin gona, ya kare al’umma daga fari, yunwa da sauran ƙalubalen rayuwa.

Haka kuma ya yi addu’ar Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Azare, Jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya, tare da bai wa shugabanni hikima da adalci wajen gudanar da al’amuran jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

Peter Obi Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Sayi Hannun Jarin Matatar Mai Ta Dangote

Bayan kammala addu’ar, an yi kira ga al’umma da su ci gaba da yawaita addu’a, istigfari da tuba, tare da kyautata mu’amala da juna, kasancewar waɗannan na daga cikin hanyoyin neman rahamar Allah da saukar ni’imominsa.

Mahalarta taron sun bayyana fatan cewa Allah Maɗaukakin Sarki zai karɓi addu’o’insu, ya saukar da ruwan sama mai albarka wanda zai amfani manoma, makiyaya da daukacin al’umma, tare da sanya albarka a cikin amfanin gona da rayuwar jama’a.

Roƙon Ruwa
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima
  • Sulaiman
    Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN
  • Sulaiman
    Peter Obi Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Sayi Hannun Jarin Matatar Mai Ta Dangote
  • Sulaiman
    Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa

MASU ALAKA

Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima
Labarai

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026
peter
Labarai

Peter Obi Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Sayi Hannun Jarin Matatar Mai Ta Dangote

September 16, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

’Yansanda Sun Kama Mutane 240 Bisa Zargin Laifuka Daban-Daban A Yobe

September 16, 2026
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

'Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026
Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

September 16, 2026
peter

Peter Obi Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Sayi Hannun Jarin Matatar Mai Ta Dangote

September 16, 2026
Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa

Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa

September 16, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 240 Bisa Zargin Laifuka Daban-Daban A Yobe

September 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

September 16, 2026
Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

September 16, 2026
Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

September 16, 2026
TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

September 16, 2026
APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa

APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.