ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Gwamnonin Kano Da Kaduna Sun Yi Gargaɗi Kan Kalaman Ƙiyayya, Labaran Ƙarya

by Bello Hamza
18 hours ago

Gwamnonin jihohin Kano da Kaduna sun buƙaci ’yan jarida da su riƙa gudanar da aikin jarida bisa ƙa’ida da gaskiya, tare da dakile yaɗuwar kalaman ƙiyayya da bayanan ƙarya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Sun yi gargaɗin cewa kai hare-hare kan ɗaiɗaikun mutane, yaɗa saƙonnin siyasa masu rarraba kai da kuma wallafa labaran da ba a tantance sahihancinsu ba, na iya raunana cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne ta bakin wakilansu a wajen ƙaddamar da littafin Digital Shift in Nigeria’s Newspaper Industry, wanda Editan Labarai na Rukunin Jaridun LEADERSHIP, Dr Sunday Isuwa, ya rubuta, a Abuja ranar Alhamis.

ADVERTISEMENT

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya wakilta, ya bayyana damuwarsa kan yadda kalaman ƙiyayya da kai hare-hare kan mutane ke ƙaruwa a harkokin yaƙin neman zaɓe.

Ya ce irin waɗannan ayyuka ba su da amfani ga dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa ya kamata gasa ta siyasa ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi jama’a, maimakon kai hare-hare kan abokan hamayya.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yusuf ya ce, “Abin da muke gani ba shi da amfani ga dimokuraɗiyyarmu, musamman yadda muke ganin kalaman ƙiyayya da mayar da siyasa ta zama kai hare-hare kan ɗaiɗaikun mutane.”

Haka kuma, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci ’yan jarida da su tabbatar da sahihancin bayanan da suke samu kafin wallafa su, tare da tabbatar da cewa rahotanninsu na bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban dimokuraɗiyya.

Uba Sani, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya wakilta, ya ce wajibi ne ’yan jarida su wuce bayar da rahoton abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin neman zaɓe, su riƙa binciken ikirari, tabbatar da gaskiyar bayanai da kuma la’akari da tasirin rahotanninsu ga zaman lafiyar ƙasa.

Ya ce, “A waɗannan zaɓuka, dole ne mu wuce bayar da rahoton abubuwan da suka faru kawai, mu zurfafa bincike, mu tabbatar da gaskiyar bayanai, sannan mu tabbatar da cewa abin da muke wallafawa yana taimakawa dimokuraɗiyya.”

Ya ƙara da cewa, “Yaƙin neman zaɓe zai ƙare. Fastocin ’yan takara za su ɓace. Tabbas, wasu ’yan takara za su yi nasara, wasu kuma su faɗi. Amma a ƙarshen komai, abin da ya fi muhimmanci shi ne wannan ƙasa tamu mai suna Najeriya.”

Gwamnan na Kaduna ya kuma nuna damuwa kan tasirin sauye-sauyen fasaha ga masana’antar jaridu, yana mai gargaɗin cewa raguwar ma’aikatan ɗakunan labarai da sauye-sauyen hanyoyin samar da jaridu na jefa wasu ayyukan kafafen yaɗa labarai cikin haɗari.

Ya buƙaci ’yan jarida da su ƙware a fannoni daban-daban na samar da labarai ta hanyar amfani da kafafen zamani, tare da rungumar sabbin fasahohi, ciki har da basirar na’ura mai kwakwalwa (AI), domin su ci gaba da kasancewa masu amfani a wannan zamani da harkokin yaɗa labarai ke sauyawa cikin sauri.

Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci
Rahotonni

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya
Ra'ayi Riga

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
Next Post
Kwamitin Kolin JKS Ya Kira Taron Manema Labarai Game Da Zaman Da Ya Yi

Kwamitin Kolin JKS Ya Kira Taron Manema Labarai Game Da Zaman Da Ya Yi

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.