ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shigo Da Fetur Ya Ƙaru Da Kashi 59.5% A Watan Mayu A Nijeriya — NMDPRA

by Abubakar Sulaiman
3 months ago
Fetur

Hukumar Kula da Harkokin albarkatun mai (NMDPRA) ta bayyana cewa yawan shigo da fetur zuwa Nijeriya ya karu da kashi 59.5 cikin 100 a watan Mayun 2026, duk da cewa buƙatar man a cikin gida ta ragu zuwa lita miliyan 46.3 a kullum daga lita miliyan 51.1 da aka samu a watan Afrilu.

A cewar rahoton hukumar na watan Mayu, yawan fetur da ake shigowa da shi ya kai lita miliyan 5.9 a rana, yayin da jimillar wadatar fetur a ƙasar ta ƙaru zuwa lita miliyan 47.4 a rana. Sai dai wannan adadi har yanzu bai kai matakin buƙatar ƙasa baki daya na lita miliyan 50 a kullum ba.

Rahoton ya nuna cewa matatar mai ta Dangote ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da fetur a cikin gida, inda ta yi aiki da ƙarfin kashi 101.25 cikin 100, ta samar da lita miliyan 44.7 na fetur a rana, tare da samar da lita miliyan 41.5 ga kasuwar cikin gida. A gefe guda kuma, matatun mai na gwamnati da ke Fatakwal, Warri da Kaduna sun ci gaba da kasancewa a rufe a duk tsawon watan.

ADVERTISEMENT

NMDPRA ta kuma bayyana cewa an dakatar da shigo da dizel daga ƙasashen waje a watan Mayu bayan matatar Dangote ta ƙara yawan samar da dizel zuwa lita miliyan 18.8 a rana. Haka kuma, wadatar man jiragen sama ta ƙaru zuwa lita miliyan 3.6 a rana, yayin da amfani da shi ya kai lita miliyan 3.1.

Hukumar ta ce ana samun ci gaba a manyan ayyukan bututun iskar gas na ƙasa, inda aikin bututun AKK ya kai kashi 94.3 cikin 100 na kammalawa. Ta bayyana alƙaluman watan Mayu a matsayin shaida ta sauye-sauyen da ake samu a ɓangaren makamashi, ciki har da ƙaruwar samarwa a cikin gida, da rage dogaro da shigo da kayayyakin mai daga waje da kuma bunƙasar tattalin arziƙi.

LABARAI MASU NASABA

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Fetur
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati
  • Abubakar Sulaiman
    Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
  • Abubakar Sulaiman
    An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

MASU ALAKA

Gwamnatin Katsina
Labarai

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati
Labarai

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
Labarai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Next Post
Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Iran Sun Zanta Ta Waya

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.