ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Michael Carrick Zai Iya Dawo Da Manchester United Hayyacinta?

by Abba Ibrahim Wada
8 months ago
Michael

Ba kamar Ɗaɓi Alonso ba a Real Madrid, an daɗe ana hasashen cewa ƙungiyar Manchester United zƙ ta kori mai horas da ƴan wasanta Ruben Amorim bayan faɗi tashin da ƙungiyar take yi a gasar Firimiyar Ingila.

Idan mai karatu bai manta ba a watan Nuwamban shekara ta 2024 ne aka naɗa Amorim a matsayin mai horas da ƙungiyar, inda ya jagoranci ƙungiyar zuwa wasan ƙarshe na kofin Europa a watan Mayun da ya gabata, inda suka yi rashin nasara a hannun Tottenham.

  • Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal
  • Babu Sihiri A Nasarorin Da Manchester City Ke Samu A Baya Bayan Nan – Guardiola

Kafin a kori Amorim, Manchester United ce ta shida a teburin Premier, duk da haka hukumomin ƙungiyar sun yi ta kawar da kai kan kiraye-kirayen sallamar kocin, har sai a wannan lokaci.

ADVERTISEMENT

A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce “wannan shi ne lokaci mafi dacewa na kawo sauyi. Hakan zai bai wa ƙungiyar damar kammala kakar gasar Premier a mataki mafi dacewa.

Sannan a cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta gode wa Ruben bisa ga gudumawar da ya bai wa ƙungiyar kuma tana masa fatan alheri a ayyukansa na gaba. Tuni ƙungiyar ta bayyana tsohon ɗan wasan ƙungiyar Machael Carrick, domin maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya zuwa ƙarshen kakar wasa.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Wace Irin Matsala Amorim Ya Samu A Man United?

Ruben Amorim ya nace wajen amfani da salon wasa na masu tsaron baya uku da ƴan wasan gefe da gefe tun bayan zuwan shi United. Amma kocin ya yi amfani da masu tsaron baya huɗu a wasan da ya samu nasara kan ƙungiyar Newcastle a washegarin Kirsimeti, kafin daga baya kuma ya koma tsohon salonsa.

Amorim ya bayyana cewa an samu saɓani tsakaninsa da shugabannin ƙungiyar game da sayen ƴan wasa. Sannan ya yi kalaman da suka nuna cewa yana samun saɓani da daraktan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Jason Wilcoɗ, kuma abin ya riƙa ƙazancewa tun bayan buɗe kasuwar musayar ƴan wasa ta wannan wata na Janairu.

 

Wane Irin Tarihi Amorim Ya Bari A United

Kafin a kore shi, Machester United na a matsayi na shida a teburin Premier bayan wasa 20, inda wasan ƙarshe suka tashi canjaras da Burnley 2-2. Wannan sakamako na nufin United ta lashe wasa ɗaya ne tal cikin wasanni biyar da ta yi a baya-bayan nan a Premier – kuma wasa uku kacal ke nan ta lashe cikin wasa 11 da ta buga a baya.

Amorim ya jagoranci Manchester United a karawa 63 jimilla, amma ya kasa yin nasara a fiye da rabin waɗannan wasanni. Ya bar ƙungiyar bayan yin nasara a wasanni 24, canjaras 18 da rashin nasara 21. Hakan na nufin ya lashe kashi 38.1% kawai na karawar United da ya jagoranta a matsayin mai horarwa.

Manchester United ta ƙare a mataki mafi muni a kan teburin Premier a matsayi na 15 a kakar da ta gabata, tun bayan da ta faɗi daga gasar a kakar wasa ta 1973 zuwa 1974, lokacin da ta faɗi daga ajin Premier zuwa ajin ƴan dagaji.

 

Shin Machael Carrick Zai Iya?

Wannan ita ce tambayar da duk wani magoyin bayan ƙungiyar yake wa kansa, domin a ƴan shekarun nan, ƙungiyar ta yi masu horarwa da dama ba tare da samun sakamakon kirki ba.

A baya Carrick, wanda ya lashe gasar firimiya guda biyar tare da gasar cin kofin Zakarun Turai a shekara ta 2008 ya taɓa horar da Manchester United shima a matsayin riƙon ƙwarya, a lokacin da ƙungiyar ta kori Ole Gunner Solkjaer, a shekara ta 2018, inda ya jagoranci ƙungiyar wasanni uku, ya yi nasara a wasanni biyu da yin canjaras a wasa ɗaya.

Yanzu dai hankali zai karkata zuwa ga tsohon ɗan wasan, wanda zai fara buga wasa da babban wasan hamayya, inda ƙungiyar ta Manchester United za ta karɓi baƙuncin Manchester City a filin wasa na Old Trafford, daga nan kuma sai ya jagoranci ƙungiyar zuwa Landan domin buga wasa da Arsenal, kafin buga wasanni biyu a gida da Fulham da Tottenham.

Michael
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
AFCON 2025: Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Morocco

AFCON 2025: Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Morocco

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.