ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Wace Ce Ainihin Barazana, Wadda Ake Takala Ko Kuma Mai Takala?

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago

A ranar 17 ga watan nan da muke ciki, wani jirgin ruwan yakin Japan mai suna “JS Ikazuchi” ya ratsa mashigin tekun Taiwan na kasar Sin, inda ya shafe kusan sa’o’i 14.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya, firaministar Japan din ta furta wasu kalamai kan yankin Taiwan, wadanda kasar Sin ta bayyana rashin amincewarta da su, ta kuma nemi Japan ta gyara kuskurenta. Sai dai maimakon kokarin gyara kuskure da neman a zauna lafiya, Japan tana ta aikata abubuwan da suka sabawa neman zaman lafiya. Wucewar wannan jirgi da ya zo a makamanciyar ranar da Japan din ta tilasta cimma yarjejeniyar da ta kai ta ga mamaye yankin Taiwan, ya nuna karara cewa takalar fada ce kawai.

Duniya na fama da tarin kalubule na yake-yake, inda wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, ke dandana kudarsu. Maimakon hada kai da sassan duniya domin yayyafawa yanayin ruwan sanyi, da alama Japan na son amfani da wannan dama wajen kara hargitsa duniya da kara nuna cewa, ba ta dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya ba.

ADVERTISEMENT

Amincewa da manufar kasancewar Sin daya tak a duniya da kasancewar Taiwan wani bangare da ba zai iya ballewa daga Sin ba, ita ce tushen dangantakar Sin da kowace kasa a duniya. Kuma dukkan kasashe sun san cewa, batun Taiwan batu ne mafi muhimmanci ga kasar Sin da bai kamata duk mai kaunar zaman lafiya ya rika takala ba.

Japan tana ta karfafa karfinta na soja a baya-bayan nan bisa abun da take kira barazana daga makwabta, amma shin wace ce ainihin baranzanar, wadda ake takala ko kuma mai takala?Ko a kutsen da Japan ta yi wa Sin shekaru 80 da suka wuce, Sin ba ta bayar da kai ba duk da illolin da kutsen ya haifar, sai ma mika wuya da Japan din ta yi daga bisani. To me ya sa Japan ke ganin za ta iya kai labari a yanzu? Ai duniya ta ci gaba, kuma kai ya waye, don haka ba za a nade hannu a kyaleta ta yi abun da ta ga dama ba.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

A matsayinsu na makwabta, kuma abokan cinikayya, kamata ya yi a ce an samu maslaha, an yi watsi da ra’ayin rikau. Tun da yanayi ya sauya, ya kamata dabaru da ra’ayi su sauya. Babu abun da matakan soja ke haifarwa sai wahalhalu da asara, kuma hakan sam ba su dace da duniyarmu ba.

Lokaci bai kure ba, Japan na iya sauya dabarunta da bin daidaitacciyar hanya domin a zauna lafiya, a ci moriya tare ta yadda al’umma da daukacin yankin za su amfana. (Faeza Mustapha)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara 

Tinubu Ya Yi Hannun-riga Da Matsalolin Da 'Yan Nijeriya Ke Ciki, In Ji Baba-Ahmed

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.