Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike wa takwaransa na kasar Switzerland Guy Parmelin sakon jaje, sakamakon bala’in gobara da ya afku a jihar Valais.
A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, ya yi matukar kaduwa da samun labarin tashin mummunar gobara a garin Crans-Montana da ke jihar Valais ta kasar Switzerland, bala’in da ya janyo babbar hasarar rayuka. A madadin gwamnati gami da jama’ar kasar Sin, Xi ya mika sakon ta’aziyya kan wadanda suka rasa rayukansu, da nuna alhini ga iyalan mamatan, tare kuma da fatan masu jin rauni za su samu sauki da wuri. (Murtala Zhang)
ADVERTISEMENT















Discussion about this post