ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin: A Sa Kaimi Ga Yunkurin Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
A man stands near the entrance of the Shangri-La Hotel, the venue for the International Institute for Strategic Studies (IISS) Shangri-La Dialogue, Asia's annual defense and security forum, in Singapore, Thursday, May 28, 2026. (AP Photo/Achmad Ibrahim)

A wajen taron tattaunawa kan aikin tsaro na Shangri-La karon 23 dake gudana a kasar Singapore, shugaban tawagar masanan rundunar kasar Sin, Meng Xiangqing ya yi wani jawabi mai taken “A sa kaimi ga yunkurin tabbatar da kwanciyar hankali a duniya”.

A cewar Mista Meng, tsarin kare tsaro a duniya na fuskantar dimbin kalubaloli, lamarin da ya sanya kasar Sin gabatar da shawarwari na karfafa tsaro a duniya, da kula da al’amuran kasa da kasa yadda ya kamata, da tsayawa kan ra’ayin tabbatar da tsaro irin na bai daya, da hadin gwiwa, wanda kuma zai dore.

Ban da haka, kasar Sin ta bukaci kasashe daban daban, da su rungumi ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da na kulawa da al’amuran duniya bisa doka, gami da kokarin kafa wani tsarin tabbatar da tsaro mai adalci a duniya.

ADVERTISEMENT

Dangane da aikin kiyaye tsarin kasa da kasa da aka tabbatar da shi bayan da aka kawo karshen babban yakin duniya na biyu, shugaban na tawagar masanan tawagar kasar Sin ya ce, ya kamata a magance farfado da ra’ayin fin karfin soja a kasar Japan. A cewarsa, kasar Japan ba ta taba kawar da mummunan ra’ayin daga tushe ba, saboda haka yana matukar shakku kan dacewar yunkurin baiwa kasar Japan damar hadin gwiwa da sauran kasashe ta fuskar aikin tsaro, da samun amincewa daga al’ummun kasa da kasa, musamman ma na kasashen Asiya da kasar Japan ta taba kaiwa hari.

Kana a yayin da yake tsokaci kan batun nukiliya, Mista Meng ya ce, kasar Sin ta bayyana ra’ayinta dangane da wannan batu sarai, kuma matsayinta bai taba sauyawa ba, wato tana tsayawa kan manufar raya fasahar nukiliya ta hanyar lumana, inda take mallakar wasu makaman nukiliya don kare kanta kadai, kuma ta yi alkawarin cewa ba za ta zama mai fara amfani da makaman ba.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Ban da haka, kasar tana son ganin an kawar da makaman nukiliya a dukkan kasashe masu makaman.Haka zalika, a gefen taron tattauna batun tsaro na Shangri-La dake gudana a wannan karo, Mista Meng ya zanta da wakilin kafar yada labarai ta CMG, inda ya yi tsokaci kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Ya ce, shugabannin kasashen 2 sun riga sun cimma matsaya daya, ta raya “dangantaka mai karko da yakini, wadda ta shafi manyan tsare-tsare” tsakanin kasashensu, abun da ya tabbatar da alkibla ga aikin raya hulda a tsakanin kasashen 2 da kuma sojojinsu. Saboda haka, ya kamata kasashen Sin da Amurka su yi kokarin hadin gwiwa da juna, don kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankunan da suke ciki, har ma a dukkanin fadin duniya baki daya. (Bello Wang)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Sojoji Sun Ceto Mutum 92 Tare Da Daƙile Harin Ƴan Ta’adda A Borno

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci