ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Mutum 92 Tare Da Daƙile Harin Ƴan Ta’adda A Borno

by Sani Anwar
3 months ago

Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK), sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su, su kimanin 92 tare da daƙile wani harin bam da aka kai a wani samame da suka yi cikin gaggawa a hanyar Buratai zuwa Kamuya a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Lt.-Col. Sani Uba, ya fitar ranar Lahadin da ta gabata.

Uba ya ce, sojojin na bataliya ta musamman ta 135 da aka tura Dutse Kura ne suka kai farmakin, biyo bayan gano ƴan ta’addan Boko Haram/ISWAP da suka yi awon gaba da mutane da motocin da suka yi garkuwa da su cikin daji a cikin kimanin awa 1122.

ADVERTISEMENT

Ya ce, nan take sojojin suka tura dakarun gaggawa tare da haɗin gwiwar runduna ta 27 ta ‘Task Force Brigade Garrison’, domin daƙile ƴan ta’addan.

Ya ce, wannan haɗaka da aka yi, ta tilasta wa maharan barin mutanen da suka yi garkuwa da su, suka gudu cikin ruɗani zuwa yankin Mangari zuwa Dora.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewarsa, an yi nasarar ceto jimillar mutane 92 da aka yi garkuwa da su, da suka haɗa da maza 52, mata 33 da yara bakwai da kuma motoci takwas.

“Ƴan ta’addan da suka tsere, a ƙoƙarinsu na jinkirta bin su, an bayar da rahoton dasa bama-bamai guda uku (IEDs) a kan hanyar Bula Zarma zuwa Mangari.”

“Ƙungiyoyin Kashe Bama-Bamai (EOD), sun amsa cikin gaggawa tare da samun nasarar kawar da duk na’urori uku, tare da share hanya don ci gaba da gudanar da ayyukansu.

“Sojoji sun yi tazarar kilomita biyar, bayan babban yankin Mangari, yayin da binciken da aka gudanar ya nuna cewa; ƴan ta’addan sun watse cikin firgici da ruɗani, inda suka yi watsi da manufar tasu,” in ji shi.

Uba ya tabbatar da cewa, ba a samu asarar ma’aikata ko kayan aiki ba, a yayin farmakin.

Ya ce, an bai wa fararen hular da aka ceto tallafin jin ƙai cikin gaggawa, sannan aka raka su Damaturu, domin ci gaba da tafiya zuwa inda suke.

A cewarsa, babban hafsan sojin ya yaba wa sojojin, bisa ƙwarewa da kuma gaggawar mayar da martani, yana mai bayyana aikin a matsayin wani nuni na ingantacciyar damar sa ido, isar da aiki da kuma shirye-shiryen yaƙi.

Haka zalika, ya nanata ƙudurin hukumar na ci gaba da matsin lamba kan ƴan ta’addan da kuma tabbatar da tsaron fararen hula a faɗin yankin Arewa-maso-gabas. 

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Tallafin Magunguna Ga Hukumar Kiwon Lafiya Ta Saliyo

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Tallafin Magunguna Ga Hukumar Kiwon Lafiya Ta Saliyo

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.