ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Maraba Da Ziyarar Aiki Da Shugaba Putin Zai Yi A Kasar

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

A yau Talata shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, zai fara ziyarar aiki a kasar Sin. Da yake amsa tambayoyi a taron manema labarai na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya bayyana cewa, Sin tana maraba da ziyarar aiki da shugaba Putin zai gudanar a kasar. A cewarsa Sin da Rasha abokan hadin gwiwa ne bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani. Ya ce a yayin ziyarar shugaba Putin a kasar Sin, shugabannin kasashen biyu za su yi musayar ra’ayoyi kan dangantakarsu da hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu duka.

A wani rahoton kuma, a ‘yan kwanakin nan, majalisun kula da Ilimi na bangarorin biyu karkashin kwamitin abokantaka da zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha sun gudanar da wani binciken jin ra’ayoyi mai taken “Abokantakar Matasan Sin da Rasha da Musayar Al’adu Tsakaninsu” ga matasa masu shekaru 18 zuwa 35 na kasashen biyu.

Sakamakon ya nuna cewa, sama da kashi tamanin cikin dari na matasan Sin da Rasha na ganin cewa, dangantakar Sin da Rasha ta abokantaka ce. Kuma dangane da haka, Guo Jiakun ya bayyana cewa, sun yi imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping da shugaba Putin, dadaddiyar abokantakar Sin da Rasha za ta kara wanzuwa a zukatan jama’a, matasan kasashen biyu kuma za su hada karfi da karfe, domin samar da kuzari ga cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Bilkisu Xin)

ADVERTISEMENT
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
Hadin Gwiwar Sin Da Afrika A Bangarori Daban Daban Na Samun Tagomashi Da Bunkasa Ayyukan Masana’antu A Fadin Nahiyar

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci