Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a Alhamis din nan cewa, kasar Sin na samarwa duniya tarin damarmaki ne ba wai haifar da matsaloli ba. Kazalika Sin ba ta takure sauran sassa, maimakon haka tana samar da damar ci gaba ne ga kowa. Sin na ci gaba da samarwa duniya karin alfanu daga kasuwanninta, da kirkire-kirkire, da ci gaba ga sauran sassa, karkashin salonta na ingiza ci gaba mai matukar inganci.
Wasu makaloli na baya-bayan nan daga masana tattalin arziki, irinsu Dani Rodrik, farfesa a jami’ar Harvard Kennedy School, da Michael R. Strain, daraktan sashen tsara manufofin tattalin arziki a cibiyar nazarin harkokin kasuwanci ta Amurka, sun yi watsi da zargin kasancewar Sin mai “Haifar da matsaloli”, da “Sin mai matse sauran sassa”.
Masanan sun amince cewa, manufofin cinikayya na Sin ba su amfanar da kasar sannan su dakile abokan hulda ba ne, maimakon haka, suna haifar da alfanu ne mai fantsama ko ina, tare da zarta batun fitar da hajojin da aka kammala sarrafawa.
Karkashin hakan ne kuma, kasar ta Sin ta zamo kan gaba wajen fitar da hajojin amfani a masana’antun sarrafa kayayyaki, da sassan na’urori, da kayayyakin da ba a kammala sarrafa su ba, wanda ta hakan take rage tsadar bunkasa masana’antu a kasashe masu yawa. Don haka, neman kasar Sin ta janye ta baiwa wasu kasashe guri, ta yadda kamfanoninta na gida za su iya durkushewa, gurguwar dabara ce a fannin tattalin arziki.
Da yake tsokaci dangane da hakan, Lin Jian ya ce, karin al’ummun kasa da kasa na bayyana ra’ayoyin makamantan na masanan. Har ila yau, kayayyakin Sin masu inganci, da rahusa, sun taimaka wajen rage tsadar bunkasa masana’antu a kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, kirkire-kirkiren kasar Sin dake a bude, kuma masu game ko ina sun samarwa karin kasashen duniya da kafar kyautata fasahohinsu na zamani. Kazalika, hajojin Sin madaidaita kuma masu karko, sun karfafa juriyar tsarin gudanar da harkokin masana’antu na duniya, sun kuma taimakawa kasashe masu tasowa, da damar neman gaggauta zamanantar da kansu. (Saminu Alhassan)














