Hukumar lura da hada-hadar dakon hajoji da sayayya ta kasar Sin, ta ce daga farkon shekarar bana zuwa yanzu, Sin ta ci gaba da fadada hanyoyin dakon hajoji ta sama, inda ta kai ga bude sabbin hanyoyin kasa da kasa 115 na dakon hajoji ta sama a sassan kasar cikin watanni takwas na farkon shekarar nan.
A bangaren adadin hanyoyin da aka bude a mabanbantan sassan duniya kuwa, an kaddamar da hanyoyi 57 zuwa sassan nahiyar Asiya, da na Turai 41, da na arewacin Amurka 13, da na Afirka 3, da kuma guda daya ta kudancin Amurka.
A bangaren hajojin da ake safararsu kuwa, akwai wadanda ake cinikayyarsu tsakanin kasa da kasa ta kafofin sayayya na intanet, da hajojin da aka sarrafa bisa manyan fasahohi, da wadanda aka karawa inganci, da na lantarki da sassan harhada motoci. (Saminu Alhassan)














