Mummunan ibtila’in zabtarewar kasa wanda ya haifar da ambaliyar ruwa da malalar laka a kasar Nepal da kan iyakar jihar Xizang mai cin gashin kai ta Sin, ya kara tunatar da duniya bukatar gaggawa da ake da ita, ta daukar matakan shawo kan matsalar sauyin yanayi wanda ke kara zama babbar barazana ga dorewar rayuwar bil’adama a dukkanin sassan duniyar nan.
Wannan ibtila’i ya sake tunatar da mu cewa, lokaci ya yi da duniya za ta dunkule waje guda domin ceto bil’adama daga halaka.Alkaluman baya bayan nan sun nuna yadda a kasar Nepal, wancan bala’i na malalar laka ya hallaka mutane 1,127, tare da wasu karin mutane 4,800 da suka bace, yayin da a jihar Xizang ta Sin mutane 16 suka rasu, wasu kuma 546 suka bace. Kazalika, akwai wasu daruruwan baki ’yan kasashe da yankuna da dama na duniya da su ma ibtila’in ya rutsa da su.
Kafin wannan bala’i ma, masana da dama sun sha kokawa game da yadda dagawar tudun ruwan teku ke kara barazana ga tsibirai dake kwari, yayin da ake fuskantar karuwar yanayin zafi a wurare da dama ciki har da Turai, yankin da a bana ya fuskanci tsananin zafi, wanda a bazarar bana ya sabbaba mutuwar sama da mutane 30,000.
Baya ga haka, sassa da dama na duniya na kara fuskantar yanayin El Niño na dumamar saman teku, wanda hakan ke haifar da karin rashin tabbas, da kara jefa rayukan jama’a cikin hadurra da kuma gurgunta daidaiton zamantakewar al’umma.Yayin da sassan kasa da kasa ke kara azamar bunkasa matakan shawo kan wannan kalubale, kasar Sin a bangarenta, ta himmatu wajen shiga, da bayar da tarin gudunmawa, tana kuma taka rawar gani wajen jagorantar tsarin ayyukan dakile sauyin yanayi a matakin kasa da kasa.
Kasar Sin ta shafe tsawon shekaru tana aiki tukuru a fannin kyautata da kare muhallin halittu, karkashin manufofinta na samar da ci gaba, har ma ta himmatu wajen kaiwa kololuwar fitar da hayakin carbon mai dumama yanayi kafin shekarar 2030, da magance fitar da shi nan zuwa shekarar 2060, da ma sauran manyan matakai da take aiwatarwa.
A matakin kasa da kasa kuwa, Sin tana goyon bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, da samar da hajoji daga fasahohi marasa gurbata yanayi, irinsu ababen hawa masu aiki da lantarki, da masu aiki da hasken rana da sauransu, wanda hakan ya yi matukar ingiza nasarar matakan shawo kan sauyin yanayi.
Tabbas, ba wani sashe na duniya da zai iya tsira daga matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa. Don haka, wajibi ne dukkanin kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen tunkarar wannan kalubale. Wannan lokaci ne da duniya ke matukar bukatar yin aiki tare, ta yadda za a kai ga gudu tare a kuma tsira tare!














