Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce gwamnatin Sin na taya shugaban Zambia Hakainde Hichilema, murnar sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu.
Lin, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce Sin na dora matukar muhimmanci ga ci gaban alakarta da Zambia, kuma a shirye take ta yi aiki da sabuwar gwamnatin Zambia, wajen kara zurfafa cikakkiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da samar da gagarumin alfanu ga al’ummun kasashen biyu.
Hichilema, ya lashe kuri’u masu amfani sama da miliyan 2.9, ko sama da kaso 50 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada, ya kuma cika ka’idar kundin tsarin mulkin kasar ta samun nasara, ba tare da bukatar kada kuri’a a zagayen zabe na biyu ba, kamar dai yadda hukumar zaben kasar ta ECZ ta tabbatar. (Saminu Alhassan)














