ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Yanke Shawarar Mika Agajin Gaggawa Ga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, Sin da kasashen Afirka ’yan uwa ne wadanda ke fuskantar mawuyacin hali tare.

Don haka game da sabon zagayen barkewar cutar Ebola a jamhuriyar demokradiyyar Kongo, gwamnatin Sin ta yanke shawarar mika agajin gaggawa ga kasar, kuma ta tura tawagar kwararrun likitoci zuwa kasar, domin samar da hidimomi da agajin kiwon lafiya.

A lokaci guda kuma, tana bayar da taimako ga kwamitin kungiyar AU, don tallafawa ayyukan kandagarki da shawo kan cutar ta Ebola karkashin cibiyar Afirka CDC.

ADVERTISEMENT

Lin ya bayyana hakan ne a gun taron manema labarai da aka gudanar a yau Litinin. Kuma a game da shirin kasar Japan na kara habaka hadin gwiwar tsaro tare da kungiyar NATO, Lin ya bayyana cewa, Sin ta nuna matukar damuwa game da matakin na Japan.

Ya ce ayyukan farfado da ra’ayin nuna karfin soja, da kuma yawaita mu’amala da rukunonin sojoji da Japan ke yi, sun karya tanadin kundin tsarin mulkin Japan, da ma dokokin kasa da kasa, kana suna kalubalantar tsarin kasa da kasa na bayan yaki, kuma sun saba wa kalaman da Japan din ta furta, na ayyana kanta a matsayin “kasa mai kiyaye zaman lafiya.”

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Bugu da kari, game da kalaman da ministan tsaron Japan ya yi a kwanan nan, Lin ya ce jerin maganganu da ayyukan da Japan ta yi a baya-bayan nan, sun haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinta, kuma dole ne al’ummar duniya su kasance masu taka tsantsan sosai game da hakan.

Game da ziyarar aiki da ministan wajen Sin Wang Yi ya gudanar a kasar Kanada a kwanan nan kuwa, Lin ya bayyana cewa, Sin a shirye take ta ci gaba da zakulo hanyoyin da za a bi, don inganta sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Kanada, da kuma habaka ci gaban dangantakar kasashen biyu, mai karko, kwanciyar hankali da dorewa.

Bugu da kari, Lin ya kuma yi bayani game da nasarar da Sin ta samu, ta kammala shugabancin kwamitin tsaron MDD na watan Mayu, yana mai cewa, Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori, tare da ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta na wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Safiyah Ma)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi
  • Sulaiman
    An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya
  • Sulaiman
    Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
  • Sulaiman
    Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

MASU ALAKA

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi
Daga Birnin Sin

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
Daga Birnin Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al’ummar Nasarawa – Wadada

Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al'ummar Nasarawa - Wadada

LABARAI MASU NASABA

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Makiyaya Sun Yi Asarar Shanu 200,000 Ta Dalilin Rikice-Rikice – MACBAN

September 13, 2026
Sin

Farashin Man Fetur Ya Sake Tashi A Abuja

September 13, 2026
Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026
Sin

Malamai Da Limamai 3,000 Sun Yi Addu’ar Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu A 2027

September 13, 2026
An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Sin

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.