ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Sauran Mutane 4 Da Aka Sace Tare Da Marigayi Janar Rabe A Katsina

by Sulaiman
3 months ago
Sojoji

Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun yi nasarar ceto wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su yayin ci gaba da farmakin da ake kai wa kan wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Muhammadu Fulani, da mabiyansa a Jihar Katsina.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na Jihar Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya sanya wa hannu kuma aka fitar da ita da safiyar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen da aka ceto sun kasance cikin waɗanda aka yi garkuwa da su tare da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DDI), Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane.

ADVERTISEMENT

Tun da farko, dakarun soji sun ceto matar marigayin, Hajiya Amina Abubakar, kafin wannan sabon samame da ya kai ga kuɓutar da sauran waɗanda suka rage.

A cewar gwamnatin jihar, waɗanda aka ceto sun haɗa da Musa Yakuba, mai shekaru 62; Alhaji Sa’adu Dayi, mai shekaru 68; Mukhtar Danja, mai shekaru 36, da Salisu Danja, mai shekaru 50.

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

Sanarwar ta ce an kuɓutar da su ne a yayin ci gaba da ayyukan soji a wuraren da ake zargin ’yan bindigar na fakewa da gudanar da ayyukansu.

Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Sojoji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Next Post
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Sojoji Sun Ceto Manoma 7 Da Aka Sace, Sun Kwato Babura Daga Hannun ’Yan Bindiga A Sokoto

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.