Masu masana’antu da suka halarci taron shekara-shekara na 54 na Ƙungiyar Masu Masana’antu ta Nijeriya (MAN), reshen Kano-Jigawa, sun yi tururuwar zuwa rumfar Kamfanin Dangote domin neman ƙarin bayani kan hannayen jarin matatarsa.
Taron na kwanaki uku ya ƙare ranar Alhamis.
Sayar da hannayen jarin, wadda za ta gudana daga 14 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Oktoba 2026, zai bai wa ’yan Nijeriya da sauran waɗanda suka cancanta damar sayen hannun jari a matatar man fetur ta Dangote.
A yayin taron, masu masana’antar sun nuna damuwa kan matsalolin da ke addabar harkokin kasuwanci, ciki har da yawan haraji, tsadar wutar lantarki, rashin isasshen ababen more rayuwa, tsadar rance, rashin tsaro, matsalar canjin kuɗin waje da kuma gasa daga kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Shugaban MAN na reshen Sharada/Challawa, Alhaji Nura S. Madugu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Jihar Kano da su rage wa masana’antu haraji tare da haɗa haraji da kuɗaɗen caji domin kauce wa biyan haraji sau biyu ko sama da haka.
Ya ce masu masana’antu na taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuma ƙara wa gwamnati kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji, baya ga tallafa wa al’ummomin da suke gudanar da ayyukansu
.Shi ma Shugaban MAN na reshen Bompai/Jigawa, Mohammed Bello I. Umar, ya yi kira da a ƙara yaƙi da fasa-ƙwauri, jabun kaya da shigo da kayayyakin da ba su da inganci, waɗanda yake cewa suna cutar da masu masana’antu na cikin gida.
Ya kuma buƙaci a samar da wutar lantarki mai ɗorewa da rahusa, tare da yaba wa matakan gyaran tsarin wutar lantarki da ake yi a Kano, yana mai kira da a gaggauta aiwatar da su domin bunƙasa masana’antu.













