Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar malaman Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) guda 3,252 da aka tantance cikin Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya, a wani mataki da ke da nufin magance ƙarancin malamai a Makarantun Haɗin Kai na Tarayya (Federal Unity Colleges) da kuma inganta ilimi.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Ikharo Attah, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar ministan, za a ba da fifiko ga malaman PTA da aka tantance, waɗanda da dama daga cikinsu suka shafe kusan shekaru 25 suna koyarwa a Makarantun Unity na Tarayya domin su zama cikakkun ma’aikatan gwamnati.
Alausa ya bayyana amincewar a matsayin wani babban mataki da gwamnatin Tinubu ta ɗauka domin ƙarfafa ma’aikatan koyarwa a makarantu, tare da karrama gudummawar dubban malaman PTA da suka ci gaba da tabbatar da ɗorewar harkar koyarwa a makarantun gwamnatin tarayya tsawon shekaru.














