An gudanar da bikin bude gadar kogin Nyong ta Kamaru, wadda kamfanin China First Highway Engineering Co., Ltd. (CFHEC) na Sin ya daukin nauyin ginawa, a Nyong-et-Kelle dake yankin tsakiyar Kamaru.
Ministan kula da ayyukan jama’a, da ministan sufuri, da ministar kula da harkokin jama’a, da sauran manyan jami’an Kamaru ne suka halarci bikin da ya gudana a jiya Laraba.
Ministan kula da ayyukan jama’a na Kamaru, Emmanuel Nganou Djoumessi, ya yaba da kwarewar Sin a fannoni kamar na gudanar da ayyukan gini, da aikace-aikacen fasahohi, da kuma kula da aiwatar da yarjejeniya.
Yana ganin cewa, gadar ba saukakawa al’ummar yankin ketare kogin Nyong lafiya kadai ta yi ba, ta kuma ba da muhimmiyar gudummawa wajen inganta ci gaban aikin noma, da habaka tattalin arzikin yankin da karfafa sadarwa da sauransu.
Gadar kogin Nyong, wadda aka fara ginawa a watan Yunin shekarar 2024, tsawonta ya kai kimanin mita 1120, kuma muhimmin aiki ne wajen kyautata tsarin hanyoyin mota a yankin.
A da, mazauna yankin galibi suna ketare kogin ne ta hanyar jiragen ruwa, wanda hakan ya kan haifar da hadurra da yawa.(Safiyah Ma)














