ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wasu Da Aka Sace A Zamfara, Katsina Da Kebbi

by Sadiq
2 months ago

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su, sannan suka daƙile yunkurin sace mutane tare da kama wasu da ake zargi da kai wa ‘yan ta’adda kayan da suka kai wasu hare-hare a jihohin Zamfara, Katsina da Kebbi.

Rundunar sojin ta ce an gudanar da waɗannan ayyuka ne a ranakun 19 da 20 ga watan Yuli a ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma.

A Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara, sojoji sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa cewa wasu ‘yan ta’adda na ƙoƙarin yin garkuwa da mutane a wani gida.

ADVERTISEMENT

Da isar sojojin, maharan suka tsere, lamarin da ya sa aka kuɓutar da mutanen da ake shirin sacewa.

A Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina, sojoji sun ceto mutum uku da suka tsere daga hannun masu garkuwa da su yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi, kuma maharan na barci.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

An sace mutanen ne a ranar 14 ga watan Yuli yayin da suke aiki a gonakinsu da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Daga bisani an miƙa su ga hukumomin da suka dace.

A Jihar Kebbi, sojoji sun tare wata mota ɗauke da babura 10 da ake zargin ana shirin kai wa ‘yan ta’adda ne.

Haka kuma, an kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da aka ƙwato baburan domin ci gaba da bincike.

Rundunar sojin ta yaba wa dakarun kan saurin ɗaukar mataki da kuma ƙwarewar da suka nuna wajen daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.

Ta kuma gode wa al’umma kan ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai, tare da buƙatar su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile ‘Yan Ta’adda Daga Karɓar Haraji A Yobe

Sojoji Sun Daƙile 'Yan Ta'adda Daga Karɓar Haraji A Yobe

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.