ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Majalisa Ta Bayar Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Hare-haren Borno

by Sulaiman
5 months ago
gaza

Majalisar Dattawa ta umurci Babban Hafsan Tsaro, Olufemi Oluyede, da sauran shugabannin hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan ayyuka da kayan aikin sojoji bayan hare-haren da aka kai kan sansanonin soji a Benisheikh da Monguno a Jihar Borno.

Umarnin ya biyo bayan wani muhimmin kudurin gaggawa da Mataimakin shugaban mai tsawatarwa na Majalisar, Tahir Monguno (Borno ta Arewa), ya gabatar dangane da sabbin hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Da yake gabatar da kudirin yayin zaman majalisar ranar Laraba, ɗan majalisar ya nuna matuƙar damuwa kan hare-haren baya-bayan nan da suka yi sanadin mutuwar jami’an soja da dama, ciki har da Birgediya Janar Oseni Braimoh, Kanal Mohammed Isya, Kyaftin A.M. Esmat, Laftanar Kelvin Festus, da wasu sojoji 13.

ADVERTISEMENT

Matsayar da majalisar ta cimmawa, ta bukaci gudanar da cikakken bincike kan yadda hare-haren suka faru, ciki har da duba ko kayan aikin sojoji sun wadatar da kuma bin ƙa’idodin aikin soja yadda ya kamata.

Yayin jagorantar muhawarar, Sanata Monguno ya nuna damuwa kan yawaitar hare-hare a Monguno, wadda muhimmiyar cibiyar soji ce, da kuma Benisheikh da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Ya ce yadda hare-haren ke faruwa na nuna cewa ‘yan ta’addan na ƙoƙarin raunana ayyukan sojoji tare da kawo cikas ga ayyukan jin ƙai da harkokin kasuwanci a yankin.

A nasa jawabin, Sanatan Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya ce halin da ake ciki a Arewa maso Gabas yana nuna irin matsalolin tsaro da ƙasar baki ɗaya ke fuskanta, yana mai gargadin cewa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da sake fardaɗowa duk da ayyukan tsaro da ake gudanarwa a kansu.

Majalisa
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Nada Kai A Matsayin Shugaban Kasar Taiwan Jawo Wa Kai Kaskanci Ne

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.