ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Sojoji Sun Kwato Dabbobi 529 Daga Hannun ‘Yan Ta’adda A Katsina 

by Sulaiman
7 months ago

Dakarun sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin Rundunar 17 Brigade a Katsina sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 da ’yan ta’adda suka sace, bayan musayar wuta da aka yi da su a Kafur, Jihar Katsina. Rundunar ta ce, an gudanar da samamen ne biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna motsin ’yan ta’adda a yankin Kasuwan Sabo.

A cewar Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Kyaftin Abayomi Adisa, dakarun FOB Malumfashi ƙarƙashin jagorancin Kwamandan sansanin, Laftanar Kanar M.M. Isa, sun kai samamen a ranar 7 ga Fabrairu, 2026, kan wasu ’yan ta’adda da ake zargin sun shigo daga Jihar Zamfara. Rahotanni sun nuna cewa an danganta jagorancin gungun yan ta’addan da Idi Abasu Aiki, wanda ake zargin ɗan’uwan fitaccen jagoran ’yan bindiga Ado Aliero ne.

ADVERTISEMENT
  • Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke Biyo Bayan Sace Iyalai A Kaduna
  • NiMet Ta Yi Hasashen Ƙwallewar Rana Da Gajimare Na Kwana Uku, Litinin – Talata

Da sojojin suka iso, ’yan ta’addan sun buɗe wuta, amma dakarun sun mayar da martani da ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa dazuzzuka tare da barin wasu daga cikin dabbobin da suka sace. Sojojin sun ci gaba da binsu tsakanin Burdugau da Unguwan Matau a Malumfashi, inda ’yan ta’addan suka ƙara watsar da sauran dabbobin.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Jimilla, an ƙwato shanu 290, tumaki 238, jaki 1, da kuma babur 1, duk da cewa shanu 14 sun mutu yayin musayar wuta bayan da ’yan ta’addan suka yi amfani da su a matsayin garkuwa. Rundunar ta ce babu wani soja da ya jikkata. An miƙa dabbobin ga hukumomin da abin ya shafa domin tantancewa da mayar da su ga masu su, tare da yabon jarumtaka da ƙwarewar dakarun daga GOC 8 Division, Manjo Janar Paul Koughna, wanda ya tabbatar da ci gaba da tsaurara farmaki domin tabbatar da tsaro a yankin.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

MASU ALAKA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
Labarai

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
Sin Ta Bukaci Takaichi Ta Janye Kalaman Da Ta Yi Kan Taiwan Na Sin Bayan Zaben Japan

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.