ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsofaffin Manyan Sakatarori Sun Karrama Gwamna Lawal, Sun Yaba Da Ayyukan Ci Gaban Zamfara

by Sulaiman
8 months ago
Zamfara

Ƙungiyar Tsofaffin Manyan Sakatarori na Jihar Zamfara ta karrama Gwamna Dauda Lawal tare da yaba wa ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa a faɗin jihar.

An miƙa masa lambar yabo ta girmamawa ne a ranar Juma’a a ɗakin taro na Gidan Gwamnati da ke Gusau, yayin wani taro da ya haɗa manyan tsofaffin jami’an gwamnati da suka yi wa jihar hidima tsawon shekaru.

ADVERTISEMENT
  • Ƙungiyar ‘Dikko Na Kowa Ne’ Ta Jinjina Wa Gwamnan Katsina Bisa Biyan Ƴan Fansho Haƙƙoƙinsu 
  • Burina Shi Ne Fito Da Daraja Da Mutuncin Matanmu Na Arewacin Nijeriya —Hajara Kabir

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ƙungiyar ta bayyana manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin Lawal ta aiwatar a matsayin dalilin ba shi wannan karramawa.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sun nuna cewa sauye-sauyen da aka samu a fannoni da dama sun sa suka ga ya dace su girmama gwamnan bisa ƙoƙarinsa.

Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon, Gwamna Lawal ya gode wa ƙungiyar bisa ganin ya cancanci wannan girmamawa, yana mai cewa babu wata karramawa da ta wuce wadda ta fito daga hannun manyan mutane da suka shafe rayuwarsu suna hidimta wa jiha cikin gaskiya da ƙwarewa.

Ya ce, duk da an shirya masa liyafar girmamawa, rashin lokaci ya hana hakan tabbata, amma hakan ba zai rage darajar wannan karramawa a gare shi ba. Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki ne bisa gaskiya da riƙon amana, kuma tun kafin hawansa mulki ya tsara manufofi shida da suka zamo tubalin jagorancin gwamnatinsa.

A cewarsa, tsaro shi ne ginshiƙin farko a cikin manufofin, kuma ana samun gagarumin ci gaba a bangaren. Ya kuma bayyana cewa ana aiwatar da ayyuka a dukkan ƙananan hukumomin jihar domin buɗe ƙofar zuba jari da habaka tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa, ana sa ran kammala aikin filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na jihar cikin ‘yan watanni masu zuwa.

Gwamnan ya bayyana cewa babu ƙaramar hukuma a Zamfara da ba a zuba sama da naira biliyan ashirin a ayyukan ci gaba ba, yana mai kira ga jama’a su duba ayyukan da ke gudana domin ganin sauyin da ake samu da idanunsu.

Haka kuma ya ce ana samun sauƙin matsalolin tsaro a hankali, yayin da kuɗaɗen shiga na cikin gida suka tashi daga kimanin Naira miliyan tamanin zuwa sama da Naira biliyan biyar.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Muhammad Bello Umar, ya ce sun yanke shawarar karrama gwamnan ne saboda irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan fara aikinta a 2023.

Ya ce tun daga farko gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwa da jajircewa ta hanyar fito da ajanda shida, wadda a cewarsa ta zarce tsammanin da dama.

Ya kuma tuna cewa a wani taronsu na baya, sun roƙi a biya bashin hakƙoƙin ritaya, kuma gwamnati ta amsa buƙatar tare da biyan sama da Naira biliyan goma sha uku da ake bin gwamnati.

A cewarsa, tarihin Zamfara ba zai manta da Gwamna Lawal ba saboda irin tasirin ayyukansa ga ma’aikata, lafiya, ilimi da sauran manyan ayyukan more rayuwa.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar Guinea Da Switzerland

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.