ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burina Shi Ne Fito Da Daraja Da Mutuncin Matanmu Na Arewacin Nijeriya —Hajara Kabir

by Leadership Hausa
8 months ago
arewa

Kamar yadda ya gabata a kundin farko (na shekarar 2010), wannan kundin na gaba ya ƙunshi jerin muƙaloli masu alaƙa da juna amma mabambanta, waɗanda ke bayani kan mata daga fannoni daban-daban na al’umma, tare da bambancin matakan nasara daga Arewacin Nijeriya. (Northern Women Development: A Historical and Contemporary Perspective on Northern Nigerian Women) yana nazartar rikitarwa da ke tattare da nasarorin da mata suka samu cikin yanayin al’adu da addini na Arewacin Nijeriya, na tarihi da na zamani.

Lokacin da ƙwararrun marubuta mata, masana da ƴan jarida irin su Hajara Muhammad Kabir suka raba zurfin fahimtarsu game da matsayin mata da nasarorinsu a Arewacin Nijeriya, suna ba masu karatu sabbin ra’ayoyi masu amfani, batutuwa da fahimta mai zurfi.

A ƙarshe, Hajara Muhammad Kabir ta bayyana cewa babban ƙalubale ga maza da mata a Arewacin Nijeriya shi ne jagorantar al’ummominmu zuwa wani sabon zamani wanda ke mutunta haƙƙokin mu na haɗin kai kuma ke rungumar addinai da al’adu daban-daban, inda ake maraba da bambancin shaidun mutum da kuma girmama su.

ADVERTISEMENT

Yana da muhimmanci a jaddada cewa wani muhimmin vangare na wannan sauyi shi ne sake fassara matsayin mata a matsayin ƴan’Adam masu cin gashin kansu, masu ɗaukar nauyi, kuma sama da komai a matsayin ƴan ƙasa da suka cancanci haƙƙoƙi iri ɗaya da damar samun ilimi, adalci, da ƴancin siyasa da tattalin arziki. Ga dai yadda hirra ta kasance kamar yadda Editanmu Bello Hamza naƙalto mana. 

  • Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Tinubu
  • Sojoji Sun Kama Mai Tsara Harin Ƙunar Baƙin Wake A Arewa-Maso-Gabas

Masu karatu za su so jin cikakken sunanki, da ƙudurin da ke zuciyarki

LABARAI MASU NASABA

Tarurrukan Daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa Cikin Tarihi (1980-2021): Guzurin Ranar Hausa ta Duniya

Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta

Ni suna na Hajara Muhammad Kabir, kuma ni marubuciya ce mai bincike a fagen ilimi.

 

Wane irin buri kike da shi a halin yanzu?

A halin yanzu na duƙufa ne wajen tattara muhimman bayanai a kan irin gudunmawar da matan arewacin Nijeriya suka bayar a harkokin yau da kullum. Kuma a irin shekarun da na shafe musamman a aikin jarida da kuma ganin cewa na bada himma ga ƙoƙarin ci gaban ilimin mata da tattara bayanan da suka shafi rawar da suka taka ko kuma in ce harkokin raya al’a’dun gargajiya, kasuwanci, jagoranci da kuma ayyukan raya al’umma a yankin baki ɗaya. Kuma kamar yadda na bayyana, ayyukan da na yi a baya sun taimaka min wajen samun ƙwarin gwiwar goge rashin fahimtar da ake yi wa mata tare da samar da kyakkyawar dama ta inganta tunaninmu da kuma irin kaifin basirar da mu mata muke da ita. Sannan irin ƙoƙarin da nake yi shi ya kai ga matakin wallafa littafi akan ci gaba ko kuma nasarar da matan arewa suka samu a cikin gida da kuma wajen ƙasar.

arewa

Wane hange kika ya kai ki ga rubuta wannan littafi?

Na ɗauki lokaci mai tsawo ina wannan tunanin, domin akwai bayanai marasa daɗi a kan matan arewacin Nijeriya, kuma hakan na faruwa ne sobada rashin wanda zai bayar da cikakkun bayanai da suka dace a kansu, sai ya zamanto ana yi musu wani irin kallo da gurguwar fahimta, hakan kuma ya ba ni damar aiwatar da bincike da tattara bayanai domin nuna darajar matanmu na arewacin Nijeriya a idon duniya. bayan wallafa littafi na farko da na yi akan matan arewa a shekara ta 2010, da kuma ganin irin tasirin da ya yi, sai na ga cewar ya kamata na ci gaba da bincike tare da wallafa littafi na biyu.

Sannan na ga dacewar ci gaba da lalubo irin nasarorin da mata suka cimma musamman matanmu na arewacin Nijeriya, da kuma ganin irin rawar da suka taka wajen tafiya da zamani bisa irin sauyi da aka samu na zamani ta fuskoki daban-daban a cikin al’umma. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne ina so na tanadar da bayanai akan matan da suka taka rawa a fagen raya al’a’dunmu da kuma bunƙasa tattalin arziki, domin ‘yan baya dake tasowa su samu madogara.

 

Waɗanne saƙonni kike son isarwa cikin littafin?

To babban saƙon da nake son isarwa ga mutane shi ne, matan arewacin Nijeriya sun daɗe suna taka rawa wajen ci gaban ƙasa a vangarori da dama, kuma wannan littafi ya kawar da duk wani soki burutsu da ake yi akan matan arewacin Nijeriya, waɗanda ake musu kallon ba su da wani tasiri ga ci gaban al’umma. Bayan haka littafin ya yi duba ga irin muhimmiyar rawa ko kuma gudunmawar da mata ke takawa ga ci gaban ƙasa musamman matanmu na arewacin Nijeriya

 

Wane irin ƙalubale kika fuskanta yayin aiwatar da wannan muhimmin aiki ?

Eh toh, ga duk wani marubuci ko marubuciya ba a rasa ƙalubale, domin aiki ne da ya ƙunshi zantawa da masana da ƙwararru da kuma waɗanda lamarin ya shafa, tattarawa da killace bayanai, bibiya da fayyace bayanai da duba vangarori mabambanta, waɗanda suka shafi ilimi, kasuwanci ko cinikayya har zuwa vangaren gwammati da al’a’du da kuma ci gaban al’umma.

Sannan wasu daga cikin ƙalubalen da aka ci karo da su sun haɗa da yadda za’a samu sahihin tarihi, da yadda za’a samar da gyara akan soki burutsu da aka yi ta yi akan mata, tare da tabbatar da ganin littafin ya kasance an samar da shi ba tare son zuciya ba. A haƙiƙanin gaskiya, tarihin arewacin Nijeriya ba zai tava cika ba tare da la’akari da tasiri da kuma irin gudunmawar da mata suka bayar a yankin ba.

 

Akwai wani tasiri da kike ganin littafin zai yi ga makarantansa?

To fatana dai shi ne duk wanda ya karanta shi musamman mata matasa su amfana da bayanan dake ciki domin ya ƙunshi tatattun bayanai na gaskiya.

Kuma zai bai wa ƴan majalisun ƙasa da masana fagen ilimi da kuma jagororin al’umma kyakkyawar alƙibla wajen samar da ci gaba sannan ina fatan wannan littafi zai yi tasiri wajen tafiyar da mata a harkokin mulki, tattalin arziki, kasuwanci da dai sauran su.

Mun gode Ƙwarai da gaske

Nima na gode

arewa
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura

MASU ALAKA

Tarurrukan Daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa Cikin Tarihi (1980-2021): Guzurin Ranar Hausa ta Duniya
Adabi

Tarurrukan Daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa Cikin Tarihi (1980-2021): Guzurin Ranar Hausa ta Duniya

August 26, 2026
Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta
Adabi

Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta

May 31, 2026
Zambar Kudi: Kotu Ta Tasa Keyar Dillalin Gidaje Zuwa Gidan Kaso
Adabi

EFCC Ta Kama Mutum 11 Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba A Kwara

February 6, 2026
Next Post

Me Ya Sa Masu Koyarwa 'Yan Asalin Ingila Ba Sa Iya Lashe Kofin Premier?

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.