ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

by Khalid Idris Doya
3 months ago

Mutane bakwai sun rasa rayukansu, yayin da wasu shida suka jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyukan Lanzai da Dosho da ke ƙaramar hukumar Darazo a Jihar Bauchi.

Rikicin ya faru ne a ranar Alhamis, inda kuma ya jawo asarar dukiya, ciki har da gidaje da kayan amfanin jama’a da suka kai darajar dubban Naira.

Yadda Rikicin Ya Samo Asali

ADVERTISEMENT

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu da ake zargin makiyaya suka kai wa manoma da ke aiki a gonakinsu hari a wajen ƙauyen Lanzai.

Bayan haka, wasu matasa daga Lanzai sun mayar da martani ta hanyar kai farmaki zuwa ƙauyen Dosho, inda makiyaya ke zaune.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

A wajen, an banka wa wasu gidaje wuta, inda aka ce kusan ruga 50 sun ƙone gaba ɗaya tare da lalata dukiyoyi da dama.

Martanin ‘Yansanda

Kakakin ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da shida suka jikkata kuma suke karɓar magani a asibiti.

Bayan samun rahoton, an tura jami’an tsaro na musamman zuwa yankin domin daƙile rikicin da kuma fara bincike kan abin da ya faru.

Bincike Da Kira A Zauna Lafiya

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin.

Ya kuma yi gargaɗi cewa duk wanda aka samu da hannu a rikicin ko ɗaukar doka a hannunsa zai fuskanci hukunci.

Hukumomi sun kuma yi kira ga shugabannin al’umma da mazauna yankin da su kwantar da hankali tare da guje wa ɗaukar doka a hannu domin kauce wa ƙarin rikici.

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Kashe Mutane 7, Ya Jikkata 6 A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.