A ranar 5 ga watan Agustan nan, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa sun sanar da daukar matakan ramuwar gayya, domin mayar da martani kan jerin matakai marasa kyau da hukumar kula da harkokin sadarwa ta tarayyar Amurka (FCC) da ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka suka dauka wadanda suka shafi kasar Sin.
Tun bayan taron shugabannin kasashen Sin da Amurka da aka gudanar a Busan a karshen watan Oktoban bara, hukumar FCC ta ci gaba da maimaita amfani da batun tsaron kasa ta hanyar da ba ta dace ba, tare da bullo da manufofi na takurawa da ke shafar kasar Sin.
Masana sun bayyana cewa, ire-iren wadannan matakai sun zama dabi’ar bangaren Amurka, wadanda aka tsara domin matsin lamba ga kasar Sin, da nufin samun damar cin gajiyarsu wajen tattaunawa; inda hakan kuma ya nuna irin fargabar da wasu jami’an Amurka ke da ita game da ci gaban kasar Sin.
Domin kyautata dangantaka bisa manyan tsare-tsare cikin kwanciyar hankali tsakanin Sin da Amurka, babban abin da ya fi muhimmanci shi ne aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Kazalika, kiyaye irin wannan dangantaka na bukatar daukar matsayi mai ma’ana dangane da gasar da ke tsakaninsu. Dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da yanayi mai fa’ida ga bangarorin biyu tare da samar da nasara ga kowane bangare.
Idan aka fuskanci bambance-bambance ko takaddama, tattaunawa cikin mutunta juna da daidaito ita ce kadai hanyar da za ta samar da kyakkyawar mafita.Hakikanin abubuwan da ke faruwa na tsawon lokaci sun nuna cewa, kasar Sin da Amurka za su ci gajiyar hadin gwiwa, yayin da kuma za su yi asara idan suka shiga takun-saka.
Dorewar kyakkyawar dangantaka mai ma’ana cikin kwanciyar hankali a tsakanin kasashen biyu za ta cika muradun duka bangarorin biyu tare da biyan bukatun duniya baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













