Wata babbar tawaga daga gwamnatin jihar Kano sun kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji ga Sarkin Musulmi Alhajin Abubakar Sa’ad III da al’ummar jihar Sakkwato
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Tofa, mai magana da yawun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya fitar a ranar talata
Wannan tawaga dai ta samu jagorancin mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo, da sakataren gwamnati Umar Ibrahim da Sarkin Rano, Muhammad Umar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Umar Doguwa da kwamishiniyara al’adu da yawon buɗe ido, Hajiya Aisha Saji da sauran jami’an gwamnati.
Sai dai tun da farko wannan tawaga ta ziyarci gidan marigayi Sardaunan Sakkwato Alhaji Abubakar Alhaji inda suka yi wa iyalan sa ta’aziyya a madadin gwamna Abba Kabir
Da yake tarbar wannan tawaga babban ɗan marigayi, Aminu Abubakar ya nuna jin daɗi da godiya ga gwamnan Kano bisa wannan karamci da suka nuna masu na kawo ziyarar ta’aziyya.
Kazalika wannan tawaga ta ziyarci Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III inda suka isar da sakon ta’aziyyar gwamna Abba Kabir Yusuf ga Sarkin Musulmin.
Haka kuma Sarkin Musulmi ya godewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf inda ya bayyana wannan ziyara a matsayin nuna ƴan uwantaka da haɗin kai mutumen Arewacin Nijeriya.
Haka kuma tawagar ta kai ziyara ga gwamnatin jihar Sakkwato inda suka ziyarci gidan gwamnati kuma suka samu tarbar mataimakin gwamnan tare da sakataren gwamnatin jihar Sakkwato
Gwamna Abba Kabir ya yi addu’ar Allah SWT ya jikan marigayi ya yafe masa kurakuran sa ya sanya Aljanna Firdausi ta zama makomar marigayi Sardaunan Sakkwato Alhaji Abubakar Alhaji
“Muna addu’ar Allah SWT ya yafe masa kurakuransa ya sanya Aljanna Firdausi ta zama makoma a gare shi, sannan ya baiwa iyalansa da Sarkin Musulmi da gwamnatin jihar Sakkwato da kuma al’ummar Sakkwato hakurin jure wannan rashi.” Inji Gwamnan
Gwamnan wanda ya bayyana marigayi Sardaunan Sakkwato a matsayin mutumin da ake girmamawa saboda gudunmawar da ya bayar a arewacin Nijeriya wanda za a daɗe ana tunawa da shi.














