Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, ya halarci taron kasa da kasa na manyan jami’ai da aka tsara, albarkacin shekarar zaman lafiya da aminci a kasar Turkmenistan. Yayin taron na ranakunan Juma’a da jiya Asabar, Peng Qinghua ya mika wasikar taya murnar gudanar da taron ta shugaba Xi ga dandalin.
Kazalika, Peng ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Dunyagozel Gulmanova, da shugabannin manyan jam’iyyun siyasar kasar, ya kuma halarci taron shawarwari tsakanin al’ummun Sin da na Turkmenistan.
Har ila yau, ya gabatarwa kasar Turkmenistan manyan manufofin cikakken zama na 4 na kwamitin kolin JKS na 20, da kuma wasikar taya murnar taron ta shugaba Xi Jinping. (Saminu Alhassan)














