ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Seychelles

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Wang yi

Memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Mr. Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Seychelles Barry Faure a jiya Litinin a nan birnin Beijing.

Yayin tattaunawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, kwanan nan gwamnatin Seychelles tare da tarin gwamnatocin kasashe kawayenta, sun soke izinin saukar jirgin saman wakilin ‘yan awaren na Taiwan Lai Ching-te a kasashensu, bisa doka da ka’ida a fili.

Har ila yau, bangaren Seychelles ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana tsattsauran matsayinsa a fili dangane da rungumar manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”. Kuma bangaren Sin yana matukar yabawa da wannan mataki. Wang Yi ya kuma yi imanin cewa, kasashe da yawa za su yi koyi da Seychelles, tare da tsayawa a bangaren adalci da daidaitaccen tarihi.

ADVERTISEMENT

Wang Yi ya kara da cewa, bangaren Sin yana son yin amfani da damar cika shekaru 50 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, don ciyar da hadin gwiwa a fannoni kamar na raya tattalin arzikin dijital, da tattalin arzikin teku, da tattalin arzikin tsibirai, da tattalin arziki na bola jari, da kuma ciyar da cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Seychelles zuwa sabon matsayi.

Ya ce bangaren Sin zai ci gaba da goyon bayan Seychelles, wajen kare ikonsa na mallakar kasa, da ‘yancin kai, da hakkokin da suka dace, da kuma goyon bayan Seychelles wajen taka babbar rawa a harkokin shiyyarta da ma na duniya baki daya.

LABARAI MASU NASABA

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

A nasa bangaren, Barry Faure ya bayyana cewa, cikin shekaru 50 da kulla alakar diflomasiyya tsakaninsu, har kullum kasar Sin ta kasance tana cudanya tare da Seychelles bisa adalci da daidaito, kuma ta ba da muhimmin taimako ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na Seychelles.

Har ila yau, bangaren Seychelles yana godiya ga hakan. Kazalika, ya sake jaddada tsayawa tsayin daka kan manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”.

Bangaren Seychelles yana goyon bayan manyan shawarwari guda hudu na raya duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, kuma yana godiya ga bangaren Sin bisa matakin soke gaba dayan haraji kan hajojin dukkan kasashen Afirka 53 da ke da huldar diplomasiyya da Sin, kuma yana fatan yin amfani da wannan manufa mai fa’idar sosai, don amfanin al’ummominsu. (Amina Xu)

Wang yi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    “Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa
  • Sulaiman
    Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya
  • Sulaiman
    Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
  • Sulaiman
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
Wang yi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa
Daga Birnin Sin

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026
Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
Next Post
Gwamnan Adamawa Ya Sauya Wa Wasu Kwamishinoni Ma’aikatu

Gwamnan Adamawa Ya Sauya Wa Wasu Kwamishinoni Ma'aikatu

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.