ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Bayani Game Da Ziyarar Aikinsa A Wasu Kasashen Afirka

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Wang yi

A jiya Litinin ne memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi bayani game da ziyarar aiki da ya gudanar a kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, da kasashen Habasha, Tanzaniya, da kuma Lesotho.

A yayin ziyararsa, Wang Yi ya yi shawarwari kan manyan tsare-tsare tsakanin Sin da AU a hedkwatar kungiyar AU, inda aka kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka ta shekarar 2026. Dangane da wannan harka, Wang Yi ya ce, kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka, muhimman matakai ne da aka dauka, tun bayan tattaunawa tsakanin shugaba Xi Jinping da shugabannin kasashen Afirka. Ya ce, “Za mu gudanar da aikace-aikace na mu’amala kimanin 600, domin kara fahimtar jama’ar kasashen Afirka kan kyakkyawan zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar”.

Haka kuma, ya ce, nasarori da ci gaban da kasashen Afirka suka samu, ya sa shi farin ciki kwarai da gaske, kana, manyan kasuwanni a kasar Sin za su samar da damammaki masu kyau ga kasashen Afirka. A yayin taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a shekarar 2024, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shirin neman zamanantarwa a manyan fannoni guda 6 bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ya ba da jagoranci ga yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Kana, abubuwan da ya ji, da kuma wadanda ya gani a kasashen Afirka, sun ba shi tabbacin cewa kasashen Sin da Afirka za su cimma makoma mai haske a fannin neman zamanantarwa.

ADVERTISEMENT

Da yake tsokaci game da yadda aka aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin FOCAC na Beijing, Wang Yi ya ce, a halin yanzu, an riga an kaddamar da shirye-shirye har kaso 90 bisa dari na sakamakon da aka cimma a yayin taron.

Ban da haka kuma, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da kasance muhimmiyar kasa da ta inganta bunkasar tattalin arzikin duniya. Tana kuma fatan ba da taimako ga kasashen Afirka wajen neman ci gaba da farfadowa. Shugabannin kasashen Afirka sun jinjinawa kasar Sin game da nasarorin da ta cimma, suna kuma sa ran zamanantar da kasar Sin zai tallafa wa kasashen Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

A yayin ziyararsa a wannan karo, kungiyar AU da kasashen da abin ya shafa, dukkansu sun fitar da sanawar hadin gwiwa da kasar Sin, inda suka nuna goyon baya ga Sin kan kare manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”. Wang Yi ya ce, lamarin da ya sake nuna cewa, shimfida dunkulewar kasar Sin baki daya ya dace da ra’ayin al’ummomin duniya, da halin da muke ciki. Kasar Sin za ta mayar da martani ga duk wani bangare daga kasashen waje, dake son tsoma baki kan batun Taiwan, da kuma tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma irin wadannan sassa ba za su cimma nasara ba. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Wang yi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Wang yi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Ƙasar Gabon Ta Ɗage Dakatarwar Da Ta Yi Wa Aubameyang

Gwamnatin Ƙasar Gabon Ta Ɗage Dakatarwar Da Ta Yi Wa Aubameyang

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.