Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, yau Laraba a birnin Beijing. Shugaba Xi ya bukaci Sergei Lavrov ya mika sakonsa na gaisuwa zuwa ga shugaba Putin.
Ya kara da cewa, a bana ake cika shekaru 30 da kulla hulda bisa manya tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha.
Yana cewa wannan muhimmiyar dangantaka dake tsakaninsu ta samu ci gaba mai inganci da kyawawan sakamako a fannoni da dama.
Ya kuma nanata cewa, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da tabbatar da aminci a tsakaninsu da marawa juna baya, da neman ci gaba na bai daya da tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata. Haka kuma su yi amfani da kusancin da suke da shi da dacewar abota a tsakaninsu, wajen zurfafa hadin gwiwa a dukkan bangarori da karfafa juriya domin samun ci gaba.
Kuma su hada hannu wajen farfado da iko da kuzarin MDD.A nasa bangare, Sergei Lavorov ya ce karkashin jagorancin shugabanninsu, dangantakar Sin da Rasha ta nuna matukar juriya yayin da ake fuskantar matsin lamba daga waje.
Ya ce kasashen suna da kyakkyawar dangantaka a fannin ciniki da zuba jari, kuma cudanya da musayar al’adu tsakanin al’ummominsu na karuwa, kana kasashen biyu na hadin gwiwa a dandaloli daban-daban kamar MDD da kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO) da kungiyar BRICS da kungiyar APEC. Bugu da kari, a jiya Talata a nan Beijing, ministocin harkokin wajen Sin da Rasha sun dora bayanan da aka bayar kan shirye-shiryen ganawar shugabannin kasashen biyu cikin wannan shekara a sikeli, tare da yin musayar ra’ayoyi mai zurfi kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, wadanda suka hada da rikicin Amurka da Iran, da halin da ake ciki a yankin Asiya da Fasifik, da kuma rikicin Ukraine.
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ba ce, halin da ake ciki yanzu a fagen kasa da kasa na da matukar rudani, kuma cutarwar da babakere da yin gaban kai ke haifarwa ta kara tsananta, sannan tsarin jagorancin duniya yana samun garambawul sosai, kana ginshikin samar da zaman lafiya da ci gaban bil’adama na fuskantar dimbin kalubale masu wuyar sha’ani.
Wang Yi ya yi bayani cewa, yayin da ake fuskantar yanayi mai sarkakiya kuma mara tabbas a duniya, Sin da Rasha sun yi tsayin daka a kan dangantakarsu a karkashin kulawa da jagorancin shugabannin kasashen biyu da suke aiwatarwa da kansu, kana hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban ya ci gaba da kasancewa mai karfi kuma cikin juriya.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Rasha, Lavrov ya ce, kasar Rasha na da muradin yin aiki kafada-da-kafada tare da kasar Sin wajen ci gaba da mu’amala mai kyau a matakin koli, da zurfafa hadin gwiwa a aikace, da cin moriyar juna, da kuma samun nasara ga kowane bangare.
Lavrov ya kara da cewa, halin da ake ciki a fagen kasa da kasa yana fuskantar dimbin kalubale masu wuyar sha’ani, kuma wasu kasashe na kokarin kafa “kananan gungu” domin taka wa Rasha da Sin birki. (Masu Fassara: Fa’iza Mustapha, Abdulrazaq Yahuza Jere)














Discussion about this post