ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Yi Musayar Sakon Taya Murna Da Shugaban Rikon Kwarya Na Gabon Game Da Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Jakadanci Tsakanin Sassan Biyu

by Sulaiman
2 years ago
Xi

Yau Asabar, 20 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musayar sakon taya murna da shugaban rikon kwarya na kasar Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema, game da cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakon, shugaba Xi ya nuna cewa, a cikin rabin karnin da ya gabata, duk da yadda yanayin da ake ciki a duniya ke ci gaba da canjawa, kasashen Sin da Gabon sun ci gaba da daukar juna daidai, kana suna goyon bayan juna, yayin da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ke kara ingantuwa, wanda hakan ya haifar da fa’ida ta gaske ga jama’ar kasashen biyu.

  • NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
  • Wani Mutum Ya Mutu Bayan Ya Cinna Wa Kansa Wuta A Yayin Da Ake Shari’ar Trump

Xi Jinping ya kara da cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Gabon, kuma yana son yin aiki tare da shugaba Nguema, don daukar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a matsayin wani sabon mafari, na ci gaba da sada zumuncin gargajiya tsakanin kasashen biyu, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa, da wadatar da abubuwan da suka shafi dangantakar abokantaka, ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kuma hada gwiwa don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da kasashen Afirka.

ADVERTISEMENT

A nasa bangaren, shugaba Nguema ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa kan bin manufar Sin daya tak, kuma ta yi imanin cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba. Ya ce kasar Gabon tana son yin aiki tare da kasar Sin, wajen ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu gaba, tare da amfanar da jama’ar kasashen biyu.

A wannan rana kuma, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Gabon Ali Akbar Onanga Y’obeghe, sun aike da sako ga juna, don taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Xi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Amurka Na Illata Al’amuran Kasa Da Kasa Da Na Shiyya-Shiyya

Kasar Amurka Na Illata Al’amuran Kasa Da Kasa Da Na Shiyya-Shiyya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.