A ranar Talatar da ta gabata ce, kwamitin shirya taron bikin Maulidi na Darikar Tijjaniyya a kowacce shekara da ke Unguwar Mile 12 Intanashinal market a Jihar Legas a karkashin jagorancin, Alhaji Dauda Tarai, dan asalin Jihar Kano, wanda ya kasance shi ne sakataren jin dadi da walwalar kungiyar ‘yan kasuwar Mile 12.
Ya jagoranci gudanar da taron bikin Maulidin Fiyaiyan Halitta Annabi Mahammadu (SAW) a wannan shekarar a Unguwar Mile 12 Intanashinal market.
Taron bikin Maulidin ya samu halartar dimbin al’ummar Musulmi mazauna yankin Mile 12 da sauran kunan da ke makwabtaka da suka hada da unguwar Ikorodu, Shagamu, Ketu, Ojota, Agege, taron Maulidin ya gudana a harabar babban masallacin Juma’a na ‘yan Darika da ke Unguwar Mile 12.
Kadan daga cikin malaman da suka samu halartar taron bikin Maulidin sun hada da babban limamin masallacin Juma’a na ‘yan Darikar da ke Mil 12, Sheikh Malam Abubakar Bn Abubakar da Sheikh Malam Abdulbasiru Banufe da Sheikh Malam Aliyu Gwambe da Sheikh Malam Rabiu, babban limamin masallacin Juma’a na ‘yan Shinkafa Mile 12 da sauran manyan malamai.
‘Yan kwamitin shirya taron bikin Maulidin sun hada da shugaban kwamitin, Alhaji Dauda Tarai da Alhaji Muktar Jabo da Alhaji Aminu Madobi da Alhaji Saminu Zarewa da Alhaji Sani mai yadi da Alhaji Hakilu Zakiru da Alhaji Sani Na Mowa Filatan da Alhaji Auwalu Cikada Kiru da Alhaji Hasan Zarewa da Ma’azu Kwamandan ‘yan agaji Mile 12 da Lukuman Sakatare da Alhaji Kabiru mai yadi Mile 12 da Alhaji Rabiu na Alhaji Usman da Alhaji Ummaru da Dan Ubale Kiru da sauran su.
A lokacin gudanar da taron bikin Maulidin, malamai sun yi wa’azi ga al’ummar Musulmi bisa ga muhimmancin yin taron Maulidi tare da bayyana tarihinsa gaba daya, sannan sha’irai suka gabatar da kasidu daban-daban.
Daga karshe, shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Dauda da sauran mambobin kwamitin suka yi jawaban godiya ga dimbin al’ummar Musulmin da suka samu halartar taron tare da yi masu fatan alheri na komawa gidajensu lafiya.














