Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa NPA, ta sanar da cewa, tana kan shirye-shiyen samar da sabon tsarin kamun Kifi, a Tekunan kasar.
A cewar hukumar, hakan na daga cikin kokarin da take yi, na kara bunkasa tattalin arzik na Teku da kuma kara fadada, hada-hadar kamun Kifi.
Shugaban hukumar Dakta Abubakar dantsoho, ya sanar da hakan, a kasidar da ya gabatar, a babban taron ci gaba bunka fannin kamun Kifi.
kungiyar ‘yanjairda da ke dauko rahotanin a Tashoshin Jiregen Ruwa ta kasa wato MARCON ta shirya taron a jihar Legas.
Dantsoho ya gabatar da kasidar ce, mai taken, “Gudunmawar da kayan aikin Tashoshin Jiregn Ruwa za su iya bayarwa, a fagen habaka fannin kiwon Kifi a kasar”. Mista Adegbite Adewumi, Mataimakin Janar Manaja da shirya tsare-tsare a NPA ne, ya gabatar da kasidar ta Dakta dantsho, a wajen taron.
Dantsoho yayi nuni da cewa, kirkiro da tsarin, zai taiamaka wajen kara fadada fannin kamun Kifi a kasar, musamman duba da yadda ake ci gaba da hbaka tattalin arziki na Teku na kasar.
Ya jaddada cewa, ana kuma sa ran, masu zaman kansu a cikin fannin, musamman a karkashin tsarin zamani na hadaka, na PPP.
Kan kayan aikin Tashoshin da za a yi amfani da su, fannin na kamun Kifin da kuma dakon kayan da suke da saurin lalacewa, shugaban ya tabbatar da cewa, NPA nak an kokarin samar da kyakyawan yani, musamman domin kula da tafiyar da manyan kaya, zuwa Tashoshin kasar.
A cewarsa, an kebe bangaren Kirikiri, domin Shirin fara wanzar da Shirin na kamun Kifin, tare da kuma samar da na’urorin sanyi, da za a rinka adana Kifin da aka kama.
Ya kuma tabbatar da cewa, an samar da wajen ajiya manyan Kwantaina, da za su rinka dakon kayan da za su iya lalacewa da wuri
Shugaban ya kuma zayyano jeren wasu kayan da ake bukata a fannin na kiwon Kifi, kamar samar da injinonin sanyi, na adana Kifin da aka kamo da sauransu.
Kazalika, dantsoho ya sanar da cewa, manyan Jirege, na shafe sa’oi 24, suna sauka a Tashoshin kasar, musamman a Tashoshin da ke a Yammacin kasar.
A jawabinsa tun da farko, shugaban kungiya Ismail Aniemu, ya bukaci gwamnonin da ke a jihohin kasar, da su zuba jari a fannin, musamman, domin a kara samar da ayyukan yi da kuma kara karfafa samar da wadataccen abinci da kara samar da kudaden shiga.
Ya yi nuni da cewa, bai kamata ace, Nijeriy ana ci gaba da rashin amfana da albakatun da ke a cikin Tekunan kasar ba
A cewarsa, fannin kamun Kifi, kamata ya yi ace, ya cike gibin da ake da shi, a bangaren bunkasa tattalin arziki na Teku
Aniemu ya nuna damuwarsa, kan rashin mayar da hankali fannin kamun Kfi a kasar, amma aka fi mayar da hankali, a fannin dogaro kan Man Fetur da Iskar Gas
Ya kara da cewa, lokaci ya yi da kasar nan, za ta kara mayar da hankali, domin kara habaka fannin na kamun Kifi a kasar.
A cewarsa, na samar da gagarumar gudunmawa, musamamn a bangaren samar da aikin yi a kasar nan.













