ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mijina Da ’Ya’yana 4 A Lokaci Ɗaya — Bazawara

by Sadiq
2 months ago

Wata bazawara, Misis Alheri Thomas, ta bayyana irin mummunan halin da ta shiga bayan da wasu ’yan bindiga suk kai hari ƙauyen Adama Dutse da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2024.

Ta ce maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 6 na safe yayin da yawancin mazauna yankin ke barci.

“Sun shigo a hankali suka kewaye ƙauyen kafin su fara harbe-harbe,” in ji ta.

ADVERTISEMENT

A cewarta, ’yan bindigar sun riƙa shiga gida-gida suna harbin mutane, yayin da wasu mazauna ƙauyen suka tsere zuwa daji domin tsira da rayukansu.

Misis Thomas ta ce ba ta gida lokacin da aka kai harin, lamarin da ya taimaka mata ta tsira da ranta.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kamata Ƴan Bindiga 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Yobe

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

Sai dai mijinta da ’ya’yanta huɗu suna cikin gida lokacin da maharan suka kai harin.

“Mijina da ’ya’yana huɗu suna cikin gida lokacin da ’yan bindigar suka kai hari. Dukkansu an kashe su,” in ji ta.

Ta kuma ce surukarta ta ga yadda aka kashe su, amma daga baya ita ma ta rasu sakamakon firgici da tashin hankalin da lamarin ya jawo mata.

Bayan kashe iyalinta, maharan sun ƙone gidansu tare da lalata dukiyoyinsu.

Misis Thomas ta bayyana harin a matsayin babban rashi da ya jefa ta cikin matsanancin damuwa da raɗaɗin zuciya.

Ta ƙara da cewa matsalar tsaro ta daɗe tana addabar yankin, amma ta ƙara tsananta a shekarar 2024, lamarin da ya sa mutane ke rayuwa cikin fargabar sake afkuwar hare-hare.

MASU ALAKA

Manyan Labarai

Sojoji Sun Kamata Ƴan Bindiga 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Yobe

July 25, 2026
Manyan Labarai

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya
Manyan Labarai

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Hauhawar Farashi Da Rashin Tsaro Ne Manyan Ƙalubalen Nijeriya — Gwamnatin Tarayya

Hauhawar Farashi Da Rashin Tsaro Ne Manyan Ƙalubalen Nijeriya — Gwamnatin Tarayya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kamata Ƴan Bindiga 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Yobe

July 25, 2026
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Fara Aiwatar Da Shirin Inshorar Lafiya Ga Jaruman Kannywood

July 25, 2026

Ku Buɗe Wuta Kan Duk Wanda Kuka Gani Ɗauke Da Bindiga – IGP

July 25, 2026
Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

Idan Aka Cire Bangaren Man Fetur Kannywood Ce Ta Fi Samar Da Aikin Yi Ga Matasa —Hamisu Iyantama

July 25, 2026
Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe

Jihohi 28 Da Abuja Na Fuskantar Hadarin Ambaliyar Ruwa —Rahoto

July 25, 2026

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

July 25, 2026

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

July 25, 2026
An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.