Sabuwar fargabar ambaliya ta mamaye al’ummomi a sassan Nijeriya bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanya jihohi 28 da Babban Birnin Tarayya (FCT) cikin jerin yankunan da ke cikin hadarin ambaliya, tana mai gargadin cewa miliyoyin mutane a Arewa da Kudancin kasar na iya fuskantar mummunar ambaliya yayin da ake ci gaba da samun ruwan sama mai karfi.
Gargadin, wanda Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar ta hannun Cibiyar Gargadin Farko Kan Ambaliya ta Kasa (National Flood Early Warning Systems Centre), ya shafi lokacin daga 19 ga Yuli zuwa 1 ga Agusta, 2026.
Hukumomin sun yi gargadin cewa ci gaba da ruwan sama, cikar kasa da ruwa, cikar koguna da kuma rashin iya daukar ruwa da magudanan ruwa ke yi na iya haddasa mummunar ambaliya ga daruruwan al’ummomi.
Ko da yake jihohin Arewa da ke bakin manyan koguna na cikin hadari, sabon hasashen ya nuna cewa jihohin Kudancin Nijeriya ma za su fuskanci barazana, musamman manyan birane, yankunan bakin teku da kuma al’ummomin da ke kusa da koguna, inda ake sa ran za a fuskanci ambaliyar gaggawa da cikar koguna.
Jihohin da aka bayyana suke cikin mafi girman hadarin ambaliya sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benuwe, Cross Riber, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Kwara, Legas, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribers da Taraba.
Gwamnatin Tarayya ta kuma bayyana wasu manyan birane da cibiyoyin kasuwanci a Kudancin kasar da ke cikin hadari, ciki har da Legas, Lekki, Ikorodu, Agege, Apapa, Eti-Osa, Ikeja, Surulere, Badagry da Lagos Island a Jihar Legas.
A yankin Kudu maso Gabas, wuraren da ke cikin hadarin ambaliya sun hada da Aba, Umuahia, Ariaria Market, Arochukwu, Onitsha, Fegge, Bridge Head, Awka, Nnewi, Nkpor, Obosi, Anambra West, Ayamelum, Omor, Nzam, Abakaliki, Afikpo, Enugu, Nsukka, Owerri da Orlu.
Haka kuma, a yankin Kudu maso Kudu, an yi gargadi ga Yenagoa, Brass, Nembe, Kaiama, Ogbia, Sagbama, Ekeremor da Kolokuma/Opokuma a Bayelsa; Fatakwal, Bonny, Okrika, Ahoada, Omoku, Eleme, Degema da Bonny Island a Ribers; Warri, Asaba, Sapele, Ughelli, Bomadi, Burutu, Patani da Escrabos a Delta; da kuma Calabar, Bakassi, Ikom, Ogoja da Ugep a Cross Riber.
Gargadin ya kuma shafi wasu al’ummomi a Akwa Ibom, Edo, Ondo, Ogun, Osun, Oyo da Ekiti, inda ake sa ran ambaliyar birane da cikar hanyoyin ruwa za su yi barazana ga gidaje, kasuwanci, gonaki da muhimman ababen more rayuwa.
A yankin Arewa ta Tsakiya, hukumomi sun yi gargadin cewa al’ummomin Lakwaja, Ajaokuta, Idah da Ibaji a Kogi; Makurdi, Agatu, Buruku, Guma da Logo a Benuwe; da kuma Minna, Mokwa, Shiroro, Suleja da Bida a Jihar Neja na cikin babban hadari sakamakon hauhawar matakin ruwa a koguna da kuma kasancewarsu a filayen ambaliya.
Hasashen ya kuma nuna cewa al’ummomin da ke bakin koguna a Yola, Mubi, Song, Ganye a Adamawa da Jalingo, Karim Lamido, Takum da Wukari a Taraba na iya fuskantar mummunar ambaliya idan ruwan sama.
Baya ga yankunan da aka bayyana suna cikin matsanancin hadari, Ma’aikatar ta sanya Adamawa, FCT, Kebbi, Nasarawa, Filato da wasu sassan Taraba cikin yankunan da ke cikin babban hadari da ke bukatar sa ido sosai.
Haka kuma, an sanya al’ummomi 531 a jihohin Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Yobe da Zamfara cikin jerin yankunan da ke cikin matsakaicin hadarin ambaliya.
Ma’aikatar ta danganta wannan hadari da yawan ruwan sama, cikar kasa da ruwa, kwararar ruwa a sama cikn kasa, cikar magudanan ruwa da kuma tashin matakan ruwa a koguna. Ta yi gargadin cewa wadannan yanayi na iya haddasa ambaliyar gaggawa, musamman a kananan wurare da manyan biranen da ke da yawan jama’a.
Ta shawarci mazauna yankunan da ke bakin koguna, filayen ambaliya, wuraren dausayi da kusa da magudanan ruwa da su kasance cikin shiri, tana mai gargadin cewa ruwa na iya zuwa cikin kankanin lokaci ba tare da wata ishara ba.
Gwamnatin Tarayya ta kuma umarci Hukumomin Ba da Agajin Gaggawa na Jihohi (SEMA), kananan hukumomi, jami’an muhalli da masu sa ido kan ambaliya a al’umma da su kara sanya ido kan koguna, gadoji, magudanan ruwa da wuraren da ke fuskantar zaizayar kasa.
An kuma shawarci al’ummomin da aka sanya cikin matsanancin hadari da su fara shirye-shiryen kwashe jama’a idan bukatar hakan ta taso, su kare marasa karfi, su guji zama ko kasuwanci a filayen ambaliya, sannan su bi duk wani umarnin gaggawa da hukumomi suka bayar.
Ma’aikatar ta yi kira da a gaggauta share magudanan ruwa, a ci gaba da sa ido kan yawan ruwan sama da matakin ruwa, tare da kai rahoton duk wata alamar samun yawaitar ruwa cikin gaggawa.
Ta kuma jaddada cewa ya kamata a rika hada hasashen ambaliya da yanayin da ake gani a wurare, yadda magudanan ruwa da koguna ke gudana, da kuma umarnin hukumomin agajin gaggawa yayin da ake ci gaba da sa ido kan sauyin yanayi a fadin kasar.














