ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 6, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hauhawar Farashi Da Rashin Tsaro Ne Manyan Ƙalubalen Nijeriya — Gwamnatin Tarayya

by Sadiq
4 weeks ago

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa hauhawar farashi da matsalar rashin tsaro na ci gaba da zama manyan ƙalubalen da ‘yan Nijeriya ke fama da su duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da tsaro da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne, ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026.

Akume ya ce gwamnati na sane da wahalhalun da wasu manufofinta suka jawo wa jama’a, amma ya jaddada cewa an inganta tattalin arziƙin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Ya ce hauhawar farashi na ci gaba da jefa mutane cikin wahala, ko da yake a cewarsa tana raguwa a hankali.

Haka kuma, matsalar rashin tsaro na ci gaba da barazana ga rayuka da sana’o’in al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508

A cewarsa, tattalin arziƙin Nijeriya ya samu ci gaban kashi 4.07 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekarar 2025, sannan ya ƙaru da kashi 3.89 cikin 100 a zangon farko na shekarar 2026.

Akume ya kuma bayyana cewa shirye-shiryen gwamnati kamar bayar da rance ga ɗalibai, tallafin kuɗi ga masu ƙaramin ƙarfi da kuma sauƙaƙa samun bashi sun taimaka wa mutane da dama.

Ya ce sama da ɗalibai miliyan ɗaya suka amfana da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), inda aka raba sama da Naira biliyan 184 domin biyan kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.

Dangane da tsaro, Akume ya ce gwamnati na ƙara ɗaukar jami’an tsaro da samar musu da ƙarin kuɗaɗe, tare da haɗa kai da maƙwabtan ƙasashe da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su riƙa bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri da suka dace, yana mai cewa tabbatar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Sakataren ya kuma yi kira ga haɗin kan ƙasa, yana mai cewa ci gaba zai fi samuws idan jama’a suka fifita haɗin kai da amincewa da juna fiye da bambance-bambancen ƙabilanci da addini.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyenta tare da neman goyon bayan ‘yan Nijeriya a zaɓen shekarar 2027 bisa sakamakon ayyukan da ta gudanar.

A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce Ranar Dimokuraɗiyya lokaci ne na girmama waɗanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya.

Ya ƙara da cewa shekaru 27 ana mulkin dimokuraɗiyya ba tare da tsaiko ba babban abin alfahari ne a tarihin siyasar Nijeriya.

MASU ALAKA

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

July 6, 2026
Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508
Manyan Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508

July 6, 2026
Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?
Manyan Labarai

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

July 5, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kaduna Da Filato

‘Yan Bindiga Sun Yi Kwanton-Ɓauna, Sun Kashe Sojoji 7 A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma 9, Sun Sace Da Dama A Birnin Gwari

July 6, 2026
Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508

Gwamnatin Kano Ta Kashe Biliyan 928 A Ayyukan Ci Gaba 1,508

July 6, 2026
Jonathan Ya Musanta Zargin Tayin Naira Biliyan 500 Domin Raba Kuri’un Kudu Maso Kudu

Jonathan Ya Musanta Zargin Tayin Naira Biliyan 500 Domin Raba Kuri’un Kudu Maso Kudu

July 6, 2026
FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

FIFA Ta Dakatar Da Aiwatar Da Hukuncin Hana Folarin Balogun Buga Wasa

July 5, 2026
Sabbin Shaidu Sun Bulla Dake Kara Tabbatar Da Ta’asar Amfani Da Sinadarai Masu Guba Yayin Da Dakarun Japan Ke Mamaya A Sassan Kasar Sin

Sabbin Shaidu Sun Bulla Dake Kara Tabbatar Da Ta’asar Amfani Da Sinadarai Masu Guba Yayin Da Dakarun Japan Ke Mamaya A Sassan Kasar Sin

July 5, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

July 5, 2026
An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

July 5, 2026
Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

July 5, 2026
Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

July 5, 2026
Kayayyakin Sin Sun Jawo Hankalin Sassan Kasa Da Kasa

Kayayyakin Sin Sun Jawo Hankalin Sassan Kasa Da Kasa

July 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.