ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
ADC

Jam’iyyar ADC ta ce manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu sun lalata rayuwar ‘yan Nijeriya a cikin shekaru uku da suka gabata.

ADC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce rahotannin baya-bayan nan na Bankin Duniya da suka nuna cewa mutane miliyan 139 a Nijeriya yanzu suna rayuwa ciki talauci a kasar, shaida ce ta tasirin manufofin gwamnati.

Jam’iyyar ta bayyana cewa akwai shaidar cewa abubuwa za su kara tabarbarewa a kasar idan aka sake zaban Shugaba Tinubu a karo na biyu a zaben 2027.

ADVERTISEMENT

“ADC na matukar damuwa da rahotannin da Bankin Duniya ya fitar kwanan nan wanda ke nuna cewa mutane miliyan 139 a Nijeriya ko kusan kashi 60 cikin dari na yawan al’umma yanzu suna rayuwa cikin talauci a kasa.

“Wannan ba abin mamaki ba ne, domin wannan mummunan yanayin sakamakon sun faru ne sakamakon manufofin tattalin arziki da suka fifita samun kudade fiye da ceto rayuwar al’ummar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

“Jam’iyyar ADC ta sha yin gargadin cewa ci gaban tattalin arziki da kara kudaden shiga, da karuwar ajiyar kudin waje da gwamnatin APC karkashin Tinubu ke ci gaba da yin murna da su ba su da amfani idan ba su haifar da ingantaccen rayuwa ga mutane ko kare hanyoyin dogaro da kai ba,” in ji jam’iyyar adawa.

ADC, wanda ta zargi gwamnatin tarayya da nuna sakaci wajen janyo kwancin tattalin arziki da matsin rayuwa a Nijeriya. Ta ce abin da kasar ke bukata shi ne, shugaban kasa wand gwamnatinsa da gaske ta fahimci yadda mutane ke ji kuma take kula da su da gaske.

“Shaidar mutane miliyan 139 da ke cikin talauci da miliyan 17 da ke hadarin yunwa shi ne sakamakon gwamnatin Shugaba Tinubu. Bisa wannan gazawa mai muni kadai, Shugaba Tinubu ya kamata ya yi tunanin yin murabus daga ofis maimakon neman sake zaben sa.”

“Abin da Nijeriya ke matukar bukata shi ne, shugaban da gwamnatinsa da suka fahimci yadda mutane ke ji kuma suke kula da su da gaske. Gwamnati da ta fahimci cewa ainihin ma’aunin kowace manufar tattalin arziki shi ne inganta rayuwar mutane ba wai kara musu wahala ba. Shugaba wanda gwamnatinsa ba ta ci gaba da jin dadin kanta yayin da take rokon mutane su ci gaba da azumi, da kuma gwamnati da ba ta azurta kanta wajen bai wa mutane tallafi.

“Shi ya sa ADC ta yi watsi da hanyoyin rage radadi na wacin gadi da martani na gaggawa da suka zama alamar manufofin tattalin arzikin APC a karkashin shirin tallafin al’umma. Ba za a iya yaki  da talauci ta hanyar kayayyakin rage wahala kawai ba. Ana iya yaki da talauci ta hanyar gina tattalin arziki da zai bai wa ‘yan Nijeriya damar samar da karin abinci, samun albashi mai kyau, da rayuwa cikin farin ciki da daraja,” in ji sanarwar.

ADC ta yi alkawarin cewa gwamnatinta za ta aiwatar da gyare-gyare da za su magance tushen yunwa, rage farashin makamashi da tabbatar da tsaron al’ummomin manoma har ma da kara yawan samar da abinci a cikin gida, da sauran abubuwa.

ADC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
ADC

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.