ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

by Rabi'u Ali Indabawa
50 minutes ago
Pakistan

Rundunar ‘Yansanda a Jihar Benuwe ta kama wasu ‘yan kasar Pakistan bakwai bisa zargin wata tafiya mai cike da rudani a Jihar Benuwe.

Da yake yi wa manema labarai bayani a Makurdi, Kwamishinan ‘Yansandan jihar, Cletus Nwadiogbu, ya ce jami’in kula da ofishin ‘yansanda na Otukpo ya samu bayanan sirri a ranar 1 ga Yuli game da wasu baki ‘yan kasashen waje da suka sauka a wani otal.

Ya ce bayan bincike, an gano ‘yan kasar Pakistan bakwai wadanda suka kasa gabatar da sahihin mutumin da suka zo wurinsa, babu wani gamsasshen bayani kan kasuwancin kayan lantarki da suka ce suka zo yi.

ADVERTISEMENT

Nwadiogbu ya bayyana cewa mutanen sun shigo Nijeriya ne daban-daban daga kasashe mabambanta kafin daga bisani su hadu a Legas, salon tafiyar da ya ce yana kama da yadda masu aikata manyan laifuka ke motsi.

Ya kara da cewa an tura su Abuja domin ci gaba da bincike, bisa zargin cewa suna da alaka da ayyukan ta’addanci.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

A wani sumame na daban, Kwamishinan ya ce dakarun Operation Zenda sun kashe ‘yan bindiga hudu da ake zargi a wani farmakin da suka kai da asubahin ranar 2 ga Yuli a maboyarsu da ke Seyoo Gbajimba a Karamar Hukumar Guma.

Ya ce an kwato bindiga kirar AK-47 da aka kera a gida, harsasai shida, wayoyin salula da kuma laya daga hannunsu.

A wannan rana kuma, jami’an B Dibision da ke Makurdi sun kwato bindigogi kanana guda hudu da aka boye cikin galan din man injin da aka rufe, a cikin motar Sharon da ta taso daga Anyigba a Jihar Kogi, bayan wani da ake zargi ya tsere daga tashar mota.

Kwamishinan ya musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun kafa shingayen tare hanya a kan babbar hanyar Makurdi zuwa Lafia, yana mai cewa wannan rahoto karya ne kuma an kirkire shi ne domin tayar da hankali.

Ya ce jami’an sintiri sun binciki dukkan hanyar kuma sun tabbatar cewa matafiya na wucewa cikin walwala ba tare da wata matsala ba.

Nwadiogbu ya kuma yi bayani kan binciken kisan Farfesa Gabriel Saawua Nyityo da kanensa a al’ummar Adaka a ranar 8 ga Yuli, inda ya tabbatar da kama babban wanda ake zargi, Abdullahi Usman, mai shekaru 23, a wani shingen binciken NDLEA da ke Lafia.

Ya ce ta hanyar hadin gwiwa da jami’an tsaro na Jihar Nasarawa, an kama wasu karin wadanda ake zargi da hannu a lamarin.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta dakile wasu laifuka da dama a wurare daban-daban, inda ta kama mutane da dama tare da kwato makamai, laya, babura guda biyu da miyagun kwayoyi da sauran kayayyaki.

Dakaru sun dakile yunkurin garkuwa da mutane da yawa a Monguno

A wani ci gaba mai alaka da haka, dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar jami’an Rundunar ‘Yansandan MOPOL sun yi nasarar dakile yunkurin garkuwa da dalibai da yawa da mayakan ISWAP suka yi a Kwalejin ‘Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC), Monguno, a Jihar Borno, da misalin karfe 1:30 na daren ranar 19 ga Yuli, 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yada Labarai na Hedikwatar Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Jihar Borno na amfani da harabar makarantar a matsayin masaukin wucin gadi ga daliban Federal Polytechnic, Monguno.

Kyaftin Goni ya ce ana zargin mayakan sun samu damar shiga harabar makarantar ne da taimakon wasu da ake zargin masu hada baki da su ne, da nufin yin garkuwa da daliban.

Ya ce jami’an tsaro da ke bakin aiki sun gaggauta bude wuta kan maharan cikin tsari da karfi, lamarin da ya dakatar da yunkurinsu, yayin da Rundunar Gaggawa ta Sector 3 (Kuick Reaction Force – KRF) ta isa makarantar domin karfafa wa jami’an da ke wurin.

A cewarsa, da suka fuskanci karfin dakarun tsaro da juriyarsu, mayakan sun gudu cikin rudani ba tare da cimma manufarsu ta yin garkuwa da daliban ba.

Goni ya bayyana cewa duk da cewa wasu sassan gine-ginen makarantar sun lalace yayin musayar wuta, jami’an tsaro tare da hadin gwiwar Rundunar ‘Yanaandan Nijeriya sun yi nasarar shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa bayan kammala farmakin, dakarun sun yi nasarar ceto tare da kwashe dalibai 46 zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno, inda aka yi musu gwajin lafiya tare da ba su kulawar da ta dace.

Ya ce an tabbatar da cewa dukkan daliban da aka ceto suna cikin koshin lafiya, kuma ba a yi garkuwa da ko dalibi guda daya ba.

Sai dai ya ce abin takaici ne cewa wasu dalibai sun rasa rayukansu bayan sun sami raunuka sakamakon harbin kai mai uwa da wabi mayakan suka rika yi a yayin musayar wuta.

Operation Hadin Kai ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu, tare da tabbatar wa jama’a cewa ana daukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayukan al’umma da kuma tsaron cibiyoyin gwamnati masu muhimmanci a fadin Arewa maso Gabas, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno.

Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke wadanda ake zargin sun taimaka wa maharan, yayin da dakaru da sauran hukumomin tsaro ke ci gaba da farautar mayakan da suka tsere.

Operation Hadin Kai ta jaddada cewa za ta ci gaba da matsa wa kungiyoyin ta’addanci lamba ba tare da sassautawa ba, tare da hana su damar gudanar da ayyukansu, rusa karfinsu, da tabbatar da cewa makarantu da sauran muhimman cibiyoyi a Arewa maso Gabas sun kasance cikin tsaro.

…An ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa dakarun sojoji sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su, sun kashe masu garkuwa da mutane biyu, sannan sun kama mutum hudu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne ko masu hadin gwiwa da su.

Har ila yau, dakarun sun kwato makamai, harsasai da wasu kayayyaki a wasu hare-hare da suka gudanar a jihohin Borno, Yobe, Benuwe da Filato.

Rahotannin ayyukan soji da NAN ta samu a ranar Lahadi sun nuna cewa dakarun Operation Hadin Kai sun ceto mata biyu da kananan yara biyu da suka tsere daga sansanin ISWAP da ke yankin Agapalawa a tsaunukan Mandara da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Rahoton ya kuma ce wata mata tare da danta, wadanda ake kyautata zaton ‘yan uwan wani mayakin ISWAP ne, sun mika kansu ga dakarun bayan sun tsere daga sansanin Gobara da ke dajin Sambisa.

A cewar rahoton, dakarun tare da hadin gwiwar Cibilian Joint Task Force (CJTF) sun kama mutum hudu da ake zargin ‘yan ISWAP ne ko masu taimaka musu a kananan hukumomin Gwoza, Gujba da Kukawa na jihohin Borno da Yobe.

Rahoton ya ce daya daga cikin wadanda aka kama ya amsa cewa yana yi wa ‘yan ta’adda leken asiri kan motsin dakarun da ke gudanar da ayyukan kawar da ‘yan ta’adda a hanyar Baga zuwa Cross Kauwa, tare da kai musu kayan tallafi.

Rahoton ya kara da cewa dakarun sun kuma dakile yunkurin mayakan ISWAP na kutsawa garin Kirawa da ke Gwoza, lamarin da ya tilasta musu barin babur daya a wurin. Daga bisani, jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ya kashe wani dan ta’adda da ke kan hanyarsa zuwa Marte.

Pakistan
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    NLC Ta Yi Barazanar Daukar Matakin Yajin Aiki Kan Albashi Mafi Karanci
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

MASU ALAKA

Pakistan
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Pakistan
Manyan Labarai

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa
Labarai

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Next Post
Pakistan

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

LABARAI MASU NASABA

Pakistan

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

July 25, 2026
Pakistan

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

July 25, 2026
An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.