ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Ta Cafke Lauyan Bogi Da Mallakar Hatimin Kungiyar Lauyoyi Ta Nijeriya Na Jabu A Legas

by Muhammad
5 months ago

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) reshen shiyya ta 2 da ke Ikoyi, Lagos, sun fara bincike kan wani da ake zargi da yin bogin lauya, John Anoruo, bisa zargin mallakar hatimin ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) na jabu.

An kama Anoruo, wanda ke jagorantar gudanar da wata cibiyar bayar da shawara kan harkokin shari’a da ilimi a yankin Ikorodu na Jihar Legas, a ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026.

A cewar EFCC cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Talata da yamma, lamarin ya samo asali ne bayan Anoruo ya shigar da ƙorafi mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Satumba, 2025, a madadin wasu kwastomominsa kan kamfanin Global West Vessel Specialist Nigeria Limited.

ADVERTISEMENT

Sai dai bincike ya nuna cewa ƙorafin da kuma wasiƙar janye ƙarar mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Maris, 2026, duk suna ɗauke da hatimin NBA na jabu, wanda Anoruo ya amsa cewa ya samo shi ne daga wata cibiyar kasuwanci da bai bayyana ba a Legas.

A yayin binciken, mutumin mai shekaru 55 ya ce duk da cewa ya samu digirin lauya a shekarar 2018 daga Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka (UNN), bai halarci Makarantar Horas da Lauyoyi ta Nijeriya ba, wadda dole ne ga duk wanda zai yi aikin lauya a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

EFCC ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano
Al'ajabi

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

August 14, 2026
Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Next Post
CGTN: Sama Da Kaso 80 Na Masu Bayar Da Amsa Sun Soki Yadda Japan Ke Komawa Ga Tafarkin Amfani Da Karfi

CGTN: Sama Da Kaso 80 Na Masu Bayar Da Amsa Sun Soki Yadda Japan Ke Komawa Ga Tafarkin Amfani Da Karfi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.