Ɗaruruwan magoya bayan Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a a ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke Kano, kan cire sunan ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin ’yan takarar zaɓen 2027.
Masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin mataimakin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Mustapha Kwankwaso, sun miƙa ƙorafi ga INEC, suna neman a dawo da sunan Gwarzo tare da gudanar da bincike kan zargin rashin bin ƙa’ida wajen sauya sunan wasu ’yan takara.
Mai magana da yawun tafiyar Kwankwasiyya, Habib Mohammed, ya kuma zargi wasu mutane da amfani da wasiƙu da kuma sa hannun da ake zargin na jabu ne wajen sauya wasu ’yan takarar ɗariƙar.
Kwamishinan zaɓe na INEC a Kano, Abdu Zango, ya ce hukumar za ta aike da ƙorafin zuwa hedikwatarta ta ƙasa domin duba lamarin.
Ya ƙara da cewa jam’iyyun da abin ya shafa suna da wa’adin zuwa ranar 24 ga watan Oktoba domin shigar da ƙorafinsu.














