ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”

by Abubakar Abba
2 months ago
Kaduna

Mata mabiya addinin Kirista da ƴan’uwansu Musulmai, sun ce mutunta ƴancin addinai ita ce hanya ɗaya tilo da za a iya wanzar da zaman lafiya a Jihar Kaduna.

Sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwar sakamakon taro da Cibiyar Sulhu Tsakanin Addinai (IMC) da ke da shalkwata a Kaduna ta shirya masu tare da tallafin ofishin jakadanci na ƙasar Jamus da ke Abuja.

Kazakila, sun bayyana cewa za a iya wanzar da zaman lafiya ne a cikin al’umominsu idan aka ƙarfafa masu giwa.

ADVERTISEMENT

Taken taron shi ne, ƙarfafa wa mata giwa domin wanzar da shugabaci, kare ƴancin Ɗan’adma da kuma ƙara ƙarfafa mulkin dimokiraɗiyya a Kaduna.

Sun sanar da cewa idan mata suka samu damar riƙe madafun iko, hakan zai ba su damar wanzar da shirye-shiyen da gudanar da ayyukan da suka shafi wanzar da zaman lafiya, a cikin al’umma.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Haka kuma sun jaddada muhimmancin ba su horo kan yadda za su wanzar da yin sulhu a duk lokacin da aka samu aukuwar wani rikici a cikin al’umma, inda kuma suka nuna kyama kan furta kalaman haddasa ƙiyayya da tunzura jama’a a tsakanin mabiya addinai.

Sun sanar da cewa akwai buƙatar a samar da shirye-shiyen koyon sana’o’in hannu a tsakanin matan da ke a jihar, domin su zama masu dogaro da kansu tare da yin magana da murya ɗaya kan lamuran da suka shafi harkokin mata.

Matan sun kuma sanar da yin aiki da koyarwar da ke a cikin litattafan Bibul da Alƙur’ani, wanda zai taimaka masu wajen kasancewa jakadun wanzar da zaman lafiya a cikin al’ummarsu.

Taron ya kuma buƙaci gwamnatin Kaduna da ta samar da tsare-tsare da shirye-shiryen tare da samar da wadatattun kuɗaɗe na wanzar da zaman lafiya, musamman ta hanyar gudanar da yin gangamin wanzar da zaman lafiya a jihar.

Sun kuma buƙaci hukumomin tsaro a jihar da su haɗa ƙarfi da karfe da mata, musamman domin a samu nasarar daƙile duk wata barazana ta rashin hankali da ka iya kunno kai a jihar.

Sun yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙirƙiro da shiye-shiryen wanzar da zaman lafiya a ɗaukacin faɗin jihar, inda kuma suka jinji wa cibiyar bisa shirya masu taron.

Taron ya kuma samu halartar manyan malaman addinin Kirita, Musulmai, ƙungiyoyi masu zaman kansu, shugabannin ƙungiyoyin matasa da abokan haɗaka.

Kaduna
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
NIMC Ta Yi Haɗin Gwuiwa Da Ma’aikatun Gwamnati Don Faɗaɗa Rajistar NIN

NIMC Ta Yi Haɗin Gwuiwa Da Ma'aikatun Gwamnati Don Faɗaɗa Rajistar NIN

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.