ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Jana’izar Ruhullah Khomeini Ta Shiga Kundin Tarihi Na Guinness

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Khomeini

A ranar Asabar ce aka fara hidimar jana’izar tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya jagoranci ƙasar na tsawon shekara 36.

An kashe shi a wasu hare-haren Amurka da Isra’ila a ƙarshen watan Fabrairun 2026.

Wannan na zuwa ne shekara 37 bayan jana’izar jagoran addinin ƙasar na farko, Ruhullah Khomeini da aka gudanar a birnin Tehran.

ADVERTISEMENT

Bayan rasuwarsa ne majalisar ƙwararrun ƙasar suka zaɓi Ali Khamenei a matsayin sabon jagodan addinin ƙasar.

Jana’izar Ruhollah na ɗaya daga cikin manyan tarukan jana’izar da aka samu yamutsi a tarihi.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

A cewar jami’an Iran, fiye da mutum miliyan 10 ne suka halarci taron jana’izar, lamarin da ya sa Kundin Adana Tarihi na Guinness ya ayyana taron jana’izar a matsayin wadda ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin duniya, idan aka kwakwanta yawan waɗanda suka halarta da yawan al’ummar ƙasar.

Duk da cewa an samu labarin tsananta jikinsa gabanin rasuwar tasa, labarin mutuwar tasa ta girgiza ƴan ƙasar da magoya bayansa da dama.

Ya rasu shekara 10 bayan juyin-juya halin ƙasar da ya kifar da gwamnatin tsohon sarkin ƙasar da ake kira Sha, tare da kafa sabon tsaron gwamnatin Jamhuriyar Musulunci, kuma ƙasa da shekara ɗaya bayan kammala yaƙin Iran da Iraƙi.

Me ya faru a wajen “bankwana” da binne gawar?

A cikin wani rahoto na musamman mai suna “Ruhollah”, da aka naɗa kan rayuwar Ayatullah Khamne’i, ya nuna hotunansa a kwanakin ƙarshe na rayuwarsa a asibiti a kashi na ƙarshe na shirin.

A cikin rotunan, an ga Khomeini na kwance a kan gadon asibiti, likitoci da ƴan’uwansa na kewaye da shi.

An ga yadda jikinsa ya yi la’asar, yana motsi cikin tsananin wahalar jinya da kuma ba ya iya magana.

Rahoton na musamman ya kuma nuna wasu lokutan da Ruhollah Khomeini ke addu’a tare da taimakon wasu mutane, a wasu wuraren kuma an ga wasu mutanen da ke kusa da shi na ƙoƙarin ciyar da shi.

Sannan an ga hotunan likitoci da makusantansa na ƙoƙarin tallafo sh.

An ƙarƙare rahoton da nuna hotunan wasu ƴan’uwansa na kuka da jimami bayan samun labarin rasuwarsa.

Ruhollah Khomeini ya rasu ne da maraicen 3 ga watan Yunin 1989, yayin da gidajen radiyo da talbijin na ƙasar suka sanar da labarin washe gari da safe.

A lokacin hukumomin ƙasar sun ayyana makokin kwana 40, kuma magoya bayansa sun nuna jimami a kan titinan ƙasar.

A lokacin da labarin rasuwarsa ya yaɗu, dandazon mutane daga sassan ƙasar daban-daban sun ɗunguma zuwa birnin Tehran domin halartar jana’izar.

A ranar 5 ga watan Yuni ne aka kai gawarsa zuwa babban masallacin Juma’a ana birnin Tehran, domin bankwana da ita.

Bayan shirya gawar cikin likkafani, an sanya ta cikin gilashi mai haske ta yadda mutane za su iya hango ta, aka kuma ɗora ta kan wani abu mai tudu ta yadda duk wanda ya shiga masallacin zai hango ta.

Hotunan da aka ɗauka ta kyamarorin da ke yawo a sama sun nuna yadda dandazon mutane suka yi wa masallacin dafifi.

Wasu na kuka wasu na bugun ƙirgi wasu na jimami, duk a cikin alhinin mutuwar tsohon jagoran addinin.

An samu labarin cewa mutane da dama ne suka suma sakamakon zafi da cunkoson jama’a a wurin taron.

Gawar ta kwana a masallacin har zuwa washe gari, inda aka ɗauke ta zuwa maƙabartar Behesht Zahra da ke kudancin birnin Tehran, domin binne ta.

A nan ne kuma dandazon mutane suka sake taruwa, lamarin da ya ci ƙarfin jami’an tsaron da ke bayar da kariya a wurin.

An tsara tafiya daga tsakiyar Tehran zuwa Behesht Zahra, kusan kilomita 30 tsakani.

Hotunan da aka ɗauka sun nuna yadda mutane suka yi dafifi a kan titin Tehran zuwa Behesht Zahra.

Motar da ta ɗauki gawarsa ta riƙa tafiya a hankali saboda cunkoson jama’a a kan titin.

Waɗanda suka shirya jana’izar sun gaza aiwatar da tsarin jana’izar kamar yadda suka shirya tun da farko saboda yawan jama’a.

Jami’an tsaro da dakarun juyin juya halin ƙasar, sun shiga domin buɗe hanya, don samar wa motar da ke ɗauke da gawar hanya.

Yayin da ake haka a kan hanya, can kuwa a garin na Behesht Zahra tuni ya cika maƙil da jama’a, wani abu da ya haifar da wahala wajen shigar da gawar zuwa maƙabartar.

Daga ƙarshe bayan da aka fahimci babu wurin da gawar za ta shiga garin ta ƙasa, hukumomi sun sake shiri, inda suka yanke shawarar ɗaukar gawar a jirgi mai saukar ungulu zuwa cikin maƙabartar kai-tsaye.

To amma duk da haka, can ma a maƙabartar mutane sun cika ta maƙil.

Yayin da jirgin ya sauka a maƙabartar, dubban mutane sun ruga da gudu domin samun damar taɓa gawar da nufin samun tabarruki.

Hotunan da aka ɗauka sun nuna yadda mutane suka tunkari jirgin da nufin taɓa gawar idan an fito da ita, lamarin da ya haifar da turmutsutsu a maƙabartar.

Jami’an tsaro da dakarun juyin juya hali sun samu nasarar ƙwace iko da gawar, tare da maida ta jirgin, inda ya sake tashi sama.

Akbar Hashemi Rafsanjani, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin ƙasar na lokacin, ya halarci wurin a cikin jirgi mai saukar ungulu, inda ya sanya idanu a lokacin da ake maido da doka da oda a maƙabartar.

Ahmad Khomeini, ɗa ga Ruhollah Khomeini, shi ma ya halarci jana’izar.

A daidai lokacin ne kuma gidan radion ƙasar, ya sanar da ɗage jana’izar domin bai wa dandazon mutane damar ficewa daga maƙabartar.

Bayan wani lokaci, jirgin da ke ɗauke da gawar ya samu damar sauka a inda ya dace, inda kuma aka samu nasarar yin jana’izar.

‘Mutum 10,200,000 ne suka halarci jana’izar’

A cewar wasu alƙaluma daga Kundin Adana Tarihi na Guinness dandazo da matsin da aka samu a wajen jana’izar ya haifar da mutuwar mutum takwas da raunata 500.

Majiyar Kundin ta ƙara da cewa adadin mutanen da suka halarci jana’izar ya kai mutum miliyan 10,200,000.

Ayatollah Khomeini, ya kasance ɗaya daga cikin mafiya tasiri a tsarin shugabanci da siyasar da kuma Addini a tarihin Iran.

Shi ne ya jagoranci juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Pahlaɓi.

Ali Khamene’i ya gaje shi a 1989, inda ya zama jagoran addainin ƙasar na biyu, kuma mafi jimawa a mulki, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara muradun ƙasar da alaƙarta da ƙasashen waje.

Magoya bayan shagabannin biyu, na kallonsu a matsayin wata alama ta ƴancin kai da turjiya daga ƙasashen Yamma, yayin da masu suka ke zarginsu da tattare duka ikon ƙasar a hannayensu.

Jana’izar Khamene’i

A yanzu haka jami’an Iran na shirya jana’izar Ayatollah Ali Khamenei

Hukumomin Iran sun ce suna sa ran samun miliyoyin mutanen da za su halarci jana’izar Ayatollah Ali Khamenei, wadda aka tsara yi cikin tsaurara matakan tsaro.

Haka kuma, yadda Mista Khamenei ya rasa ransa ya sa jana’izar za ta ɗauki wata alama ta musamman.

A bayanan da suke yi, jami’an gwamnatin Iran da magoya bayansa na bayyana shi a matsayin ”Shahidi”, wata kalma mai ɗauke da tarin daraja a Addinin Musulunci.

Khomeini
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Khomeini
Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Khomeini
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Khomeini
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Fafutukar Neman Sabon Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.