ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIMC Ta Yi Haɗin Gwuiwa Da Ma’aikatun Gwamnati Don Faɗaɗa Rajistar NIN

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta ƙara ƙarfafa haɗin gwuiwa da manyan ma’aikatun gwamnati domin hanzarta aiwatar da sabuwar Dokar NIMC ta 2026, faɗaɗa rajistar Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da kuma bunƙasa amfani da tsarin shaidar dijital a shirye-shiryen gwamnati da ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu.

Babbar Daraktar Hukumar NIMC, Abisoye Coker-Odusote, ta gudanar da tarurruka daban-daban a Abuja da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris; da Ministan Harkokin Agaji, Dakta Bernard Doro; da Ƙaramin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Owan Enoh. Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan faɗaɗa tsarin shaidar dijital na Nijeriya, ƙarfafa kariyar bayanai, inganta ayyukan gwamnati da kuma ƙara amfani da NIN a dukkan shirye-shiryen gwamnati da masu zaman kansu.

A yayin taron, Mohammed Idris ya yaba wa shugabancin NIMC bisa abin da ya kira gagarumin ci gaba da hukumar ta samu a cikin shekaru uku da suka gabata. Ya bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya miliyan 136 sun riga sun yi rajista a kundin shaidar ɗan ƙasa, amma ya ce har yanzu miliyoyin mutane ba su yi rajista ba. Saboda haka, ya buƙaci NIMC ta ƙara ƙaimi wajen kai rajistar zuwa matakin ƙananan hukumomi ta hanyar haɗin gwiwa da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), wadda ke da ofisoshi a dukkan ƙananan hukumomin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Ministan ya jaddada cewa tsarin shaidar dijital na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofin ƙasa, aiwatar da gyaran tattalin arziki da tabbatar da kowa ya amfana da shirye-shiryen gwamnati. Ya kuma yabawa NIMC bisa yadda ta kare bayanan da ke cikin kundinta ba tare da rahoton wata matsalar satar bayanai ba, tare da tabbatar da cewa ma’aikatun da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai, ciki har da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da NOA, za su ci gaba da tallafa wa hukumar wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin yin rajistar NIN.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Yadda Jana'izar Ruhullah Khomeini Ta Shiga Kundin Tarihi Na Guinness

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.