Gwamnatin Zimbabwe da hadin gwiwar asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF), sun kaddamar da wani shirin shekaru biyu da Sin ta bayar da kudin gudanar da shi, da nufin karfafa tallafa wa farfadowa yara daga mummunan tasirin farin da sauyin yanayi na El Nino ya haifar a shekarar 2023 zuwa 2024 a kasar.
Cikin wani jawabi da aka karanta a madadinsa, a bikin kaddamar da shirin da ya gudana jiya Juma’a a asibitin Kowoyo na gundumar Goromonzi da ke lardin Mashonaland na gabashin Zimbabwe, ministan lafiya da kula da yara na kasar Douglas Mombeshora, ya gode wa gwamnatin Sin bisa goyon bayan da take ci gaba da Zimbabwe a kokarinta na shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi.
Ya ce shirin zai taimaka wajen samar da tallafin da ya hada da na ababen gina jiki da ruwa da tsaftar muhalli da jiki da kariya ga yara da kuma sauya tunani don taimaka wa al’ummomin da ibtila’in ya shafa farfadowa daga mummunan tasirin farin da El Nino ya haifar, da kuma kara musu karfin jure damuwar da matsalar yanayi ka iya haifarwa a nan gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














