ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
1 day ago
Salati

To, waɗansu malamai suka ce menene ma’anar “gayyu” wannan rufi? Suka ce ma’anarsa, idan mutum ya yi zunubi, za’a ɗiga baƙin ɗugo a cikin zuciyarsa. In za a rubuta masa zunubi, sai ɗayan Mala’ikan ya ce, ” tsaya tukunna, wata ƙila zai nemi gafara. To in baka nemi gafara ba har lokuta da yawa suka shige, shikenan sai yace “to ya za’ayi?” Rubuta, amma rubuta ɗaya. To shikenan sai ya ɗiga ma baƙin ɗugo a cikin zuciyar. Amma in mutumin nan ya tuna cewa, ya yi zunubi wata rana, sai ya nemi gafara, shi kenan sai Mala’ikan nan ya goge abin da ya ɗiga, amma duk yadda za a goge ba zai koma kamar yadda yake a baya ba. Misali, idan aka ɗiga baƙin tawada akan farin kaya, in an sanya sabulu an wanke, zai fita amma ba zai koma kamar yadda yake a baya ba, zai iya barin gurbi. To wannan zunubi ya wanke. Amma gurbinsa zai iya zama yana nan. 

To haka, ana ɗigawa ana wankewa, gurbi yana nan har sai zuciya ta zama baƙin ƙirin da wannan gurbi, ba zunubi bane amma gurbinsa ne. To shi kuma wanke wannan gurbi, sai an yi amfani da sanpefa.

Komai yana da irin na shi sanpefar da ake goge shi, har tsatsar zuciya, amma sanpefar zuciya, itace ambaton Allah, “wa saƙalatul ƙalbi zikirullahi”. To, ƙila wannan shi ne “gayyu”.

ADVERTISEMENT

Malamai sun ta yin magana akan wannan gayyu. Amma Manzon Allah SAW, Allah ya kiyaye shi da irin wannan, wannan irin gairun sauran bayi ne. Shi kuma Manzon Allah na sa na haske ne SAW. To, Manzon Allah yace ana rufi a zuciyata. “Fa astagfirullaha fil yaumi sab’ina marratan, Har sai na yi istigifari a rana sau 70. Sannan inji wannan rufi ya yaye. Muslim ne ya fitar da wannan hadisi. 

Wani hadisi yazo cewa Manzon Allah yana yin 100. Abu Dauda ya fitar da shi. Imamul Bukhari ya fitar da hadisi daga Abu Huraira radiyallahu anhu. Manzon Allah SAW yace “wallahi na rantse da Allah inni la astagfirullaha, ni ina neman gafaran Allah “wa atubu ilai” ina tuba zuwa gare shi “aksara min sab’ina” yafi 70 ma. Ni kullum sai na yi istigifari yafi 70. yanzu don wani bawan Allah yazo yace mun wannan, “wani hadisin yace 70. Wani hadisin yace 100. Wani hadisin yace yafi 70. To ku rike 100”. Menene laifin sa? Menene laifin sa a ciki? To shi yasa mu ka rike 100, koyi da Manzon Allah SAW. To ko ba komai cikin istigifari, wannan ya ishe mu.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Toh, ina fata Allah ya amfanar da mu da wannan, kuma Allah ya sa mu shiga cikin ƙungiyar masu salatin annabi SAW. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadin wa sallim. 

Toh, salati ga Manzon Allah (SAW). Babban salatin ƴan Tijjaniya, salatul Fatihi, amma kowanne irin salati ka yi, in dai akwai “wa’ala a’lihi wa sallim”, to ya karɓu.

Falala irin ta salatin Annabi SAW, ta wuce tunanin mutum, domin Allah ne da kansa yake yi, da cewarsa, “Innallaha wa mala’ikatahu, yusalluna alan nabi – Ubangiji kansa da mala’ikunsa, su da kansu suna yi wa Manzon Allah salati”.

Yanzu akwai wanda zai ce ka bar wannan? Ba wata ibada da Allah ya raƙa wa kansa sai wannan. Ba wata ibada da Allah ya ke yi, sai salati ga Manzon Allah (SAW), sannan ya kira muminai suma su yi, “ya ayyuhallazina amanu sallu alaihi wa sallimu taslima – ya ku muminai, ku yi salati a gare shi, kuma ku amintar da shi amintarwa. Zancen guda ɗaya, ya wajaba a rayuwa, ko kuwa sai kaza da kaza, wannan duk zancen iyayen mu ne fakihai, mu bar musu kayansu. Kawai dai, mu yi ta salati ga Manzon Allah (SAW) ba adadi.

Ya zo a hadisi, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Man salla alaiyya marratan wahidatan, sallallahu alaihi biha ashran – duk wanda ya yi min salati guda ɗaya, Allah zai yi masa goma”. Toh yanzu da ake ta rikici akan falalan salati kaza da kaza, yanzu waye zai iya auna salatin Allah guda ɗaya, a ajiye ragowan taran?

Toh yanzu, duk wanda ya ce, “Allahumma salli ala Muhammadin wa sallim ko Allahumma salli ala Muhammadin wa ala alihi wa sallim”, Allah ya yi masa goma.

Wannan hadisin, anan ake yanke shi, Amma akwai waɗansu ruwayoyi da suka zo da cigaba, inda suke cewa, “wanda ya yi min ɗaya, Allah zai yi masa goma. Wanda ya yi min goma, Allah zai yi masa ɗari. Wanda ya yi min ɗari, Allah zai yi masa dubu. Wanda ya yi min dubu, kafaɗarsa da kafaɗa, za ta yi gogayya wurin shiga Aljanna. Mun gode wa Allah, wannan kyauta ce ta Manzon Allah (SAW). Ai tun daga salati ɗaya ma, ai an gama shiga Aljanna.

A nan shiga Aljanna an gama, amma dai Manzon Allah ya ce wanda ya yi dubu, kafaɗa da kafaɗa za mu shiga Aljanna. Toh, salatun batijjane, in ma ba zai yi kowanne salati ba, irin abinda Shehunnai ke cewa, kasalallen batijjane, shi ne wanda kawai wuridin lazimi yake kawai yake yi. Amma ya dace, matukar ba karatun Ƙur’ani yake yi ba, ko ba neman kuɗi yake yi ba, toh, ya yi ta salati ga Manzon Allah (SAW). Toh, wai in kawai ka yi ɗari da safe, ka yi ɗari da yamma, ka yi hamsin a cikin wazifa, sannan kuma ka yi goma sha biyu (jauharatul kamali), waɗannan in ka auna adadin su, sai ka ga duk batijja ne a sati kawai, yana salatin Manzon Allah 1840.

Wannan adadi a sati ɗaya kawai, wai har in bai kara ko ɗaya akan lazimin sa ba kenan. 

Shehu Tijjani, ya tambayi Manzon Allah (SAW), “Ya Rasulallahi, an ruwaito wani hadisi, an ce ka ce, duk wanda ya yi salati gare ka, Allah zai ba shi ladan yaƙi karɓaɓɓe ɗari huɗu. Shi kuwa duk yaƙi karɓaɓɓe guda ɗaya, ka ce Allah zai bai wa mutum ladan Hajji da Umara ɗari huɗu.” Ya Rasulallahi kai ka faɗi wannan hadisi? Manzon Allah SAW ya ce ni na ce, Ya Ahmadu. Ya ce, “Toh, ya Rasulallahi, yanzu in mutum ya yi salatul Fatiha ma, za a ba shi ladan yaƙi karɓaɓɓe ɗari huɗu, wanda kowanne yaƙi ɗaya yana daidai da ladan Hajji da Umara ɗari huɗu?” Manzon Allah ya ce, “Ba haka ba ne. In mutum ya yi salatul Fatihi, sai an ba shi ladan yaƙi karɓaɓɓe ɗari huɗu sau dubu ɗari shida.”

Mu rike salatul fatihi kwarai da gaske. Shehu Tijani yana cewa, ki koyawa mutane salatul fatihi, zasu mutu a kan imani. Duk mai yinta ba zai mutu ba sai da imani. Don haka take da maƙiya a wannan zamani, ace kaza, ace kaza, kowa ma ya faɗa abinda ya ga dama. Mu dai mu rike ta. Don mu mutu da imani.

 Alhamdulillah, salatul Fatihi ɗin ɗan ɗariƙar Tijjaniya, mai izini ce, shehu nai sunce kuma ta mai izini, in ya karanta sau ɗaya, za ta yi ta maimaita kanta, har tashin kiyama. Mun gode Allah. To wannan salatin Annabi kenan, akwai maganganu da yawa akansu, wanda za a iya ɗaukar lokaci mai yawa ana maganganu akansa.

Ya isa dai, Annabi SAW yace wanda ya yi masa salati dubu, zai shiga Aljanna tare da shi, kafaɗa-da-kafaɗa. To, mun gode Allah. Ita kafaɗar Annabi SAW ba irin tamu ba ce.

Wani wawa a kasar mu, yace “ƙaddara wanga yayi dubu, wanga yayi dubu, wanga ma yayi dubu, to shi na ukun wata kafada zai kama”? Wannan tsantsar wauta ce, da jahilci, kuma raina Annabi Muhammad ne sallallahu sallam. Yanzu, idan gidan suna yaɗa labarai, mutum ɗaya ne yake zaune a studio akan kujera yake karantawa, amma TƁ nawa a faɗin duniya take haska wannan mai labaran? Waye ya san adadin miliyoyin TƁ da aka haska mai labaran? Kuma kowace TƁ ga wannan mai labaran.

Salati
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Next Post
Ganduje Ya Musanta Jita-jitar Komawa NDC

Ganduje Ya Musanta Jita-jitar Komawa NDC

LABARAI MASU NASABA

Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

Wakilin CMG Ya Zanta Da Mataimakin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu

July 4, 2026
CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

July 4, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

July 4, 2026
Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

July 4, 2026
Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

July 4, 2026
Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

July 4, 2026
Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

July 4, 2026
Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

July 4, 2026
Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC

Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC

July 4, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.