ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Salatut Tasbihi

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 months ago
Falalar

Bature ma ya yi wannan, sai Annabi SAW ne Ba zai iya wannan kudura ba, sai Allah ne kawai zai iya wannan kudura. Kowa ma zai iya wannan kudura, don haka, za mu shiga Aljanna kafada da kafada tare da Annabi SAW, insha Allahu.

To, wannan salatin Manzon Allah kenan. Bayan shi, sai mu ce, “subhana rabbika rabbil izzati ammayasifun, wasalamun alal mursalin, walhamdulillahi rabbil alamin”. Wannan kalma tazo Allah yana cewa, “fasabbihuhu bukrata wa asila – ku rika tasbihin ubangiji safiya da yamma”. Bukhari ya ruwaito hadisi cewa, “mafificiyar magana, subhanallahi walhamdulillahi wala’ilaha’illallah, Allahu Akbar”, wannan itace mafificiyar magana.

Ko in kai surutu da yawa a waje ko kai gulma a waje ko ka fadi zunubi a waje sai kai tsoron abin da ka aikata, in ka tashi za ka bar wurin, sai kace, “subhanallahi walhamdulillahi wala’ilaha’illallah, Allahu akbar”, shikenan duk an zubar da zunuban, yanzu ka dawo kamar baka yi komai ba. To, wannan kenan.

ADVERTISEMENT

Sannan Manzon Allah ya koya mana yadda ake yin salatul tasbihi, yayin da yake yi wa Ammunsa Abbas bayani. Salatul tasbihi, wacce akafi sani da salatul Ammun nabiy.

Wata rana, Abbas yazo masallaci, ba a lokacin da ake shiga masallaci ba, sai aka sanarwa Annabi SAW cewa, “ga Ammunka, a masallaci, ba kuma lokacin sallah ba”, sai yace wani abu ya kawo shi. A ce masa ya shigo. Manzon Allah SAW ya ce, baba me ya faru? Kazo ba lokacin sallah ba, yace dana, rayuwarmu na tuna ta baya a jahiliyya. Zamanin jahiliyya na tuna da abubuwan da muka yi. Naga duk kasa ta yi min kunci, sai naga kamar Allah ba zai karbe mu ba. Shine na san ba wanda zai yaye min wannan, sai Allah, sai kai (Ya Rasulallahi) . Shi yasa na taho wajen ka.

LABARAI MASU NASABA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

 Manzon Allah yace baba bana baka kyauta ba, baba ba zai yi ma baiwa ba, baba bana baka alheri ba, yace bani dana, ai dama don haka nazo. Yace idan lokacin nafila yayi, ka tashi ka yi sabuwar alwala, ko kana da alwala ka sake sabuwar alwala yanzu. In dai lokacin nafila ne. Ka tashi ka yi sabuwar alwala. Sannan, ka tada nafila. Bayan kace Allahu akbar, ka karanta Fatiha da abunda Allah ya saukake maka na Alkur’ani. Sannan ka ce subhanallahi walhamdulillahi wala’ilaha’illallah, Allahu akbar, kafa goma sha biyar (15), sai kayi ruku’u. Sai kace subhanallahi walhamdulillahi wala’ilaha’illallah, Allahu akbar goma 10. Sai ka dago, ka fadi goma (10). Kai sujada, ka fadi goma (10). Ka zauna, ka fadi goma (10). Ka kuma yin wata sujada, ka fadi goma (10), ka kuma tasowa ka zauna, ka fadi goma (10). Sannan sai ka tashi tsaye. Sai ka kuma irin haka, har sai kayi raka’a hudu. Yace baba in kai wannan in zunubin ka ya kai yawan rairayin sahara, Allah ya zubar ma da shi. Baba in kai wannan in zunubin ka ya kai kumpar  teku, Allah ya zubar ma da shi.

To da wannan, shehunnai sukan horo, Manzon Allah yace in zaka iya kai kullum, in zaka iya kai kowace juma’a, in zaka iya kai duk wata, in zaka iya duk shekara, in ma bazaka iya ba a rayuwarka ka yi guda daya. Ya isar maka. To wannan, salatul tasbihin tana da falala kwarai da gaske. Sun ce yana daga cikin falalar sa, bayan an zubar da zunubin, kudi da tarin dukiya suna zuwa.

To sai la’ilaha’illallah. Kur’ani yana cewa, “fa’alam annahu lailahaillallah – ka sani cewa, babu wani ubangiji sai Allah.

To Manzon Allah yace in mutum yace la’ilaha’illallah ya kiyaye jinin sa da dukiyarsa, sai dai da hakkin shari’a – in sun kashe a kashe su, hukuncinsu kuwa yana kan Allah, yana wajen Allah. Ba ruwa na. Duk zunubin da za su yi, sunan su murtaddai, masu laifi. Yanzu duk laifinsu na wajen Allah. In Allah ya so ya yi musu hukunci, in yaso ya gafarta musu. Don haka, babu wani abu da yafi zikirin “La ilaha illa Allah” girma.

Da yawa, akwai masu fadar “La ilaha illa Allah” amma ba sa son manzon Allah, ba su son addinin manzon Allah ba, ba su son karatu ba, suna cewa wai mutum kafiri ne. Annabi ya ce duk wanda ya ce “La ilaha illa Allah” ya kiyaye jininsa da mutuncinsa da dukiyarsa a waje na.

Kuma ya zo a hadisin “La ilaha illa Allah” da Aba Zarril-gifari, Manzon Allah SAW yake cewa, “Man kala La ilaha illa Allah” duk wanda ya ce “La ilaha illa Allah, wajaballahu al-jannah, al-jannah ta wajaba a gare shi”.

Aba zarr ya tashi ya tsuguna ya ce, “Ya Rasulallahi, wa in zana wa sarak, ko ya yi zina, ko ya yi sata?” Manzon Allah SAW ya ce, “Wa in zana wa sarak – ko da ya yi zina ko sata.” Ya ce “Ya Rasulallahi, wa in zana wa sarak?” Manzon Allah ya ce, “Wa in zana wa sarak.” “Ya Rasulallahi, wa in zana wa sarak?” A na uku, Manzon Allah ya ce, “Wa in zana wa sarak ‘ala ragmi anfi Abazar, ko ya yi zina, ko ya yi sata, a bisa turmutsa hancin ka, sai ya shiga Aljannah”.

To, wannan hadisi, Annabin musulunci ne ya fada aka rawaito. Annabi ba wai shike nan ya nuna mana hanya mu yi ta laifi bane. Mutanen badar, Allah ya ce, “Ku tafi, Allah ya gafarta muku, sun yi laifi?” A’a, Allah ya ce duk abinda ‘yan badar suka yi, ba zai cuce su ba. Manzon Allah ya ce, duk abinda Usman ya yi, ba zai cuce ce shi ba. Su Sayyadina Abubakar duk an ba su Aljannah, amma hakan bai sa sun bar addini ba ko kuma sun kama hanyar sabo. Wannan kawai ana fada mana falalar “La ilaha illa Allah” ne. Ma’ana, abu ne mai girma.

Wani hadisi kuma game da girman “la’ilaha’illallah”, hadisin manya-manyan litattafai din nan guda 99 da kuma ‘yar takardar nan da Tirmizi ya fitar da ita a hadisin, “Wani mutum zai zo a ranar alkiyama, ya tarar da manya-manya litattafai, kowane littafi daya ya toshe mahudar rana duka.

Allah ya ce ka san su? Ya ce, “Na san su ya ubangiji. Kana musun wani abu?” Ya ce, “Ko daya.” “Ai babu wani ja, a kaini wuta shikenan.” Allah ya ce, “A’a kana da wata ajiya a wajena.” Ya ce, “Ai kuma Allah sabida kankantar ajiyar ma ban ganta ba.”

Kuma wannan karamar ajiya, ya zata rinjaye wadannan manyan littattafai? Allah ya ce, “Ni bana zalunci.” Manzon Allah ya ce, “Sai Allah ya fito da wata takarda, kamar fiffiken fara.” Akwai “La ilaha illa Allah” a rubuce a ciki.

Sai Allah ya ce kana da wannan? Ya ce, “Ya ubangiji, kai dai adali ne amma me wannan zata yi?” Allah ya ce, “A’a, sai na gwada.” Ai ni ne “La ilaha illa Allah.”

Sai a dora manya-manya littafan nan a kan sikeli, sai a dora ‘yar takardar nan kamar fiffiken fara, in ji hadisi. Amma sai ta rinjaye wadannan manya-manyan littattafan, in ji Manzon Allah SAW.

To, kuma an rawaito mana wani hadisi daga Manzon Allah SAW wanda kuma babu bugun juna tsakanin su da wannan. Manzon Allah yake cewa, “Mumini zai zo a auna masa kayan sa a ranar tashin kiyama, sai mumini ya gigice, ya yi ta bincike, ya yi ta binciken kaya.”

Sai Allah ya ce, “Ni, me kake nema ne?” Ya ce, “Allah, abin da ya fi muhimmanci ni ban gani shi ba.” Ya ce, “La ilaha illa Allah ko?” Sai ya ce, “Kwarai” amma ban ganta cikin kaya na ba.” Allah ya ce, “Ai wannan ta fi karfin wani sikeli.”

Ya zan yi in dora wannan a kan sikeli. To, malamai sun ce wannan hadisin bai sauke wancan ba. Kila wannan ana nufin “La ilaha illa Allah” ta wutirin musulmi. Waccan kuma Manzon Allah ya ce, “In mutum mumini ne.”

Akwai wasu bayin Allah, su “La ilaha illa Allah” ta su, ba a takarda aka rubuta ta su ba, cikin zuciyar su aka rubuta ta.

Yadda zaka iya rubuta “La ilaha illa Allah” a takarda ka je ka dora kan injin fotosta, ka sa farar takarda a kasa, ka danna, sai “La ilaha illa Allah” din nan a sake rubuto ta acikin farar takardar nan, to Allah yana da wadansu irin bayi, in Allah ya hada ka da su, sai su yi ma fotosta ta “la ilaha illallah” a zuciyarka.

Allah ya sa mu daga cikin wadannan.

Akwai wanda za a iya auna tasa, amma akwai “La ilaha illa Allah” wacce ta fi karfin a auna.

To, wannan shi ne lambar, girman “La ilaha illa Allah”. “La ilaha illa Allah” ba ta faduwa, “La ilaha illa Allah” Allah kenan tabaraka wa ta’ala.

To Alhamdullilahi, dan darikar Tijjaniyya, Kullun, zai yi dari da safiya, dari da yamma, dari a wazifa, dari uku kenan a kullun, wannan fa, banda sauran zikirin sa fa da yake yi. In ka buga dari uku sau bakwai, kullun asati, yana da “La ilaha illa Allah” dubu biyu da dari daya.

To, banda kuma ta zikirin juma’a.

Falalar
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

MASU ALAKA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

September 4, 2026
Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
Dausayin Musulunci

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

August 28, 2026
Falalar
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

August 21, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.