ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Sule Ya Halarci Ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy, Ya Ƙara Jaddada Aniyar Jawo Masu Zuba Jari

by Zubairu M Lawal and Sulaiman
1 month ago
Gwamna Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya halarci bikin ƙaddamar da Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy a birnin Nanchang na lardin Jiangxi, a Kasar Sin, inda ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da jawo manyan masu zuba jari domin bunƙasa masana’antu da ƙara darajar albarkatun ma’adinan jihar Nasarawa.

Gwamnan ya halarci bikin tare da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, inda ya bayyana ƙaddamar da katafaren kamfanin a matsayin wani muhimmin ci gaba da zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin kamfanonin ƙasar Sin da jihohin Nijeriya masu albarkatun ma’adinai.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Sule ya yabawa shugabannin kamfanin bisa amincewar da suka nuna ga Nijeriya, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari ta hanyar aiwatar da manufofi masu gaskiya, inganta ababen more rayuwa da kuma tabbatar da gudanar da harkokin hakar ma’adinai bisa ƙa’ida.

ADVERTISEMENT

Ya ce manufar gwamnatinsa ita ce ƙarfafa kafa masana’antun da za su riƙa sarrafa albarkatun ma’adinai a cikin Jihar Nasarawa maimakon fitar da su a ɗanye, domin ƙara musu daraja, samar da ayyukan yi ga matasa, inganta musayar fasaha da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar da na ƙasa baki ɗaya.

Jajircewar gwamnatin Sule wajen inganta yanayin zuba jari ta fara haifar da sakamako, inda manyan kamfanonin ƙasar Sin suka fara kafa masana’antun sarrafa lithium a jihar. A shekarar 2024, Kamfanin Avatar New Energy ya ƙaddamar da masana’antar sarrafa lithium mai ƙarfin sarrafa tan 4,000 a kowace rana.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Haka kuma, a ranar 2 ga Yuli, 2026, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da katafaren Kamfanin Diamond New Energy da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, wanda aka gina kan jarin dala miliyan 250 na Amurka. Kamfanin na da ƙarfin sarrafa tan 6,000 na lithium a kowace rana, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masana’antun sarrafa lithium a Afirka.

Baya ga waɗannan, akwai wasu kamfanonin hakar lithium da dama da ke gudanar da ayyukansu a Jihar Nasarawa, lamarin da ya ƙara tabbatar da matsayin jihar a matsayin cibiyar masana’antar ma’adinai a Nijeriya.

A yayin ziyarar da ya kai Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy, Gwamna Sule da tawagarsa sun zagaya sassa daban-daban na kamfanin, inda suka shaida yadda ake amfani da sabbin fasahohi wajen sarrafa kayayyaki tare da bin ƙa’idojin tabbatar da inganci.

Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da irin ci gaban fasahar da ya gani, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da kamfanonin ƙasar Sin tare da neman rattaba hannu kan ƙarin yarjejeniyoyin fahimtar juna domin faɗaɗa damar zuba jari a fannonin ma’adinai da masana’antu.

A ƙarshen bikin, shugabannin Kamfanin Jinlide•Qiangyu New Energy sun karrama Gwamna Abdullahi Sule da lambar yabo ta musamman saboda gudummawar da yake bayarwa wajen ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da kuma jawo masu zuba jari zuwa Jihar Nasarawa.

Masu lura da al’amura na ganin cewa ci gaba da zuwan irin waɗannan manyan masana’antun zai taimaka wajen mayar da Jihar Nasarawa cibiyar sarrafa lithium da sauran muhimman ma’adinai a Nijeriya, tare da samar da dubban ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.

Gwamna Sule
Zubairu M Lawal
+ posts Bio
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    2027: Miyetti Allah Ta Yi Barazanar Ƙauracewa APC Kan Ci Gaba da Tsare Boɗejo
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Samar Da Abinci Mai Gina Jiki: Gwamna Sule Ya Duba Gonakin Shinkafa A Jangwa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda Ya Tallafawa Manoma Da Kayan Aikin Gona Na Miliyoyin Naira A Nasarawa
Gwamna Sule
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Martani Game Da Yiwuwar Kara Kudaden Da Amurka Ke Kashewa Da Nufin Dakile Tasirin Kasar Sin

Sin Ta Yi Martani Game Da Yiwuwar Kara Kudaden Da Amurka Ke Kashewa Da Nufin Dakile Tasirin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.