ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kada A Bar Kasashe Masu Tasowa A Baya A Zamanin AI

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago

Lokacin da injuna suka fara tunani, yaya dan adam zai yi mu’amala da su? Lokacin da fasahar AI ta fara yanke shawara, yaya za a tabbatar da tsaro? Lokacin da fasaha ta kalubalanci da’a, yaya za a daidaita matsalar? Lokacin da gibi ya fadada tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, ta yaya za a iya tabbatar da cewa kowa ya ci gajiyar fasahar?

Babban taro na duniya kan fasahar kirkirarriyar basira wato AI, wanda kuma shi ne taron inganta tsarin shugabancin duniya a bangaren AI na gudana a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda wakilan gwamnatocin kasashen duniya, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, da manyan masana kimiyya da shugabannin kamfanoni suka hadu, domin neman amsoshin tambayoyin da dan adam ke fuskanta a wannan zamani.

Kasancewarta muhimmiyar fasahar da ke jagorantar sabon juyin juya hali na fasaha da sauyin masana’antu, yanzu haka AI tana matukar canza rayuwar dan adam da tsarin ci gaban zamantakewar al’umma. Duk da haka, matsalar rashin daidaito na ci gaba na kara tsananta. Ga yawancin kasashe masu tasowa, babban kalubale a gare su shi ne yadda za su sami damar raya fasahar AI da kuma amfani da ita. Wani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa, gibin da ke tsakanin kasashe masu kananan kudin shiga da masu manyan kudin shiga na karuwa a fannin mallakar tsare-tsaren sarrafa bayanai. Har wa yau, rahoton Cibiyar Bayanai ta Afirka ya nuna cewa, an fi samun cibiyoyin sarrafa bayanai na duniya a kasashe masu ci gaba, yayin da na Afirka bai kai kashi 1% ba. Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nanata a kwanakin baya cewa, karfin AI na hannun wasu kasashe da kamfanoni kalilan, kuma kasashe masu tasowa ba su fito da muryarsu yadda ya kamata ba a tsarin jagorantar harkokin AI. Ta la’akari da irin wannan yanayin, wannan taro yana da ma’ana ta musamman ga kasashen Afirka.

ADVERTISEMENT

A bikin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi, inda ya bayyana karara cewa, “dole ne a taimaki kasashe masu tasowa wajen karfafa kwarewarsu, a kawar da gibin da ke tsakaninsu da manyan kasashe a fannin amfani da AI, a guji haifar da sabon rashin adalci a fagen AI.” Ya kuma sanar da wasu matakai na tallafawa ci gaban AI a duniya, wato nan da shekaru 5 masu zuwa, za a ba da damarmakin horo na musamman kan AI guda 5,000 ga kasashe masu tasowa, kuma za a gina cibiyoyin hadin gwiwar AI na duniya ga kungiyar ASEAN, da kungiyar Larabawa, da kungiyar Tarayyar Afirka, sai kuma kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da kuma kasashen BRICS. Har wa yau, za a samar da hidimomin tsarin gargadin mummunan yanayi na “Mazu” a kasashe 30.

Abin da ya fi jan hankali shi ne, a lokacin taron na wannan karo, an kaddamar da kungiyar hadin gwiwar AI ta duniya (WAICO), inda kasashe 29 suka zama membobin da suka kafa ta, ciki har da kasashen Afirka 10. Wannan babban mataki ne da Sin ta dauka don amsa kiran kasashe masu tasowa da kuma hada kawunan al’ummomin duniya wajen raya fasahar AI da kuma inganta tsarin shugabancin duniya ta bangaren amfani da fasahar, wato ta hanyar amfani da fa’idar Sin a fannin ci gaban AI, kuma ta hanyar samar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, ana neman yin musayar fasahohi da inganta kwarewar kasashe, domin kasashe masu tasowa su canja daga masu karbar dokoki zuwa masu tsara dokoki.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Matakan Sin sun jawo martani sosai daga kasashe masu tasowa. “Ga kasashen Afirka, bude wa juna kofa ta fannin fasahohi da hadin gwiwar nazarin kimiyya da horar da kwararru suna da matukar muhimmanci.” In ji Farfesa Abdon Atangana, masanin kimiyya na Cibiyar Kimiyya ta Duniya kuma shugaban kwamitin nazari da kirkire-kirkire na kungiyar nazarin ilmin lissafi ta Afirka. Ya kara da cewa, “muna fatan ganin kungiyar WAICO ta zama dandali mai muhimmanci na hadin gwiwar kasa da kasa, don bai wa kasashe masu tasowa damar shiga cikin harkokin kirkire-kirkiren AI da kuma tafiyar da harkoki masu alaka daidai gwargwado.” Har wa yau, Blade Nzimande, ministan kula da harkokin kimiyya da kirkire-kirkire na Afrika ta Kudu, ya yaba wa manufar ra’ayin Sin na gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama da goyon bayanta ga dukkan kasashe su shiga a dama da su cikin harkokin raya da kula da fasahar AI. A cewarsa, kasashen Afrika ba su da abubuwan da ake bukata na raya fasahar AI, kuma Sin tana samar da yanayi mai dacewa na ba kasashe masu tasowa damar cin gajiyar ci gaban fasahar AI .

Daga samar da horo zuwa inganta karfin sarrafa bayanai, daga samar da dandali zuwa shawarwari da kasa da kasa kan dokokin da za a kafa, kasar Sin na daukar hakikanan matakai don amsa tambayar da dan Adam ke fuskanta a zamanin AI, wato ya kamata a bude kofa ga kowa wajen shugabancin fasahar AI, a maimakon a dora ta a hannun wasu kasashe kalilan. Lokacin da wakilan kasashen Afirka suka sanya hannu kan yarjejeniyar WAICO a Shanghai, abin da duniya ta gani ba wai kawai kafuwar wata sabuwar kungiyar kasa da kasa ba ne, sauyi ne da ya shiga tarihi a fagen shugabancin duniya a bangaren amfani da AI. Daga nan kasashe masu tasowa sun zamanto masu tsara dokoki a maimakon masu karbarsu. Tabbas ba abu mai sauki ba ne, amma an nuna wa duniya wata alkibla, wato kasashe masu tasowa na cimma burinsu na tabbatar da makomar AI mai adalci ga kowa.

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • Sulaiman
    Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ra’ayin Sin Game Da AI Mai Mayar Da Hankali Kan Bukatun Dan Adam Ya Samu Goyon Bayan Kasa Da Kasa

Ra’ayin Sin Game Da AI Mai Mayar Da Hankali Kan Bukatun Dan Adam Ya Samu Goyon Bayan Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.