ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa Shida Da Ya Kamata Mace Ta Sani Kafin Ta Yi Aure

by Abubakar Sulaiman and Bilkisu Tijjani
2 months ago

Aure wata ni’ima ce daga Allah Maɗaukakin Sarki, kuma yana buƙatar shiri, ilimi da fahimtar hakikanin rayuwar aure. Ga wasu muhimman abubuwa guda shida da ya kamata kowace mace ta sani kafin ta shiga rayuwar aure.

1. Jin daɗi ba ya tabbata a kullum:

Rayuwar aure ba ta ƙunshi jin daɗi kaɗai ba. Akwai lokutan farin ciki da kuma lokutan ƙalubale. Idan mace ta fahimci tun kafin aure cewa rayuwar aure tana da daɗi da rashin daɗi, hakan zai taimaka mata wajen samun kwanciyar hankali da haƙurin fuskantar ƙalubale.

ADVERTISEMENT

A lokacin da aka samu rashin jituwa ko wani yanayi marar daɗi, ba za ta yi gaggawar ɗora laifi a kan mijinta ba. Haka kuma ba za ta sa ran mijinta zai kasance yana faranta mata rai ko biyan dukkan buƙatunta a kowane lokaci ba, domin babu wani ɗan Adam da yake cikakke.

2. Dangin mijinki suna da muhimmanci,

LABARAI MASU NASABA

Goron Juma’a

GORON JUMA’A 22-05-2026

Iyaye da dangin miji suna da matsayi mai girma a rayuwar aure. Saboda haka, yana da kyau mace ta yi mu’amala da su cikin girmamawa, haƙuri da kyakkyawar zuciya.

Kada ki bari abin da mutane ke faɗa game da su ya rinjayi ra’ayinki. Ki ba su damar da za ki san su da kanki. Musamman iyayen miji, su ne sanadin zuwan mijinki duniya, don haka suna da haƙƙin girmamawa.

Idan mace tana zaman lafiya da mijinta amma tana cikin saɓani da danginsa, hakan na iya shafar zaman aurensu a gaba.

3. Ba kullum za ki ji yanayin soyayya ba:

Soyayya tana sauyawa gwargwadon yanayin rayuwa. Akwai lokutan da mace za ta ji kamar ba ta cikin yanayin soyayya, amma hakan ba yana nufin ta daina son mijinta ba.

Saboda zama tare a kullum da kuma shagulgulan rayuwa, irin wannan yanayi yana iya faruwa. Muhimmin abu shi ne a ci gaba da mutunta juna, yin kyakkyawar mu’amala da ƙoƙarin sabunta soyayya a tsakanin ma’aurata.

4. Saɓani wani ɓangare ne na rayuwar aure:

Babu gidan aure da ba a samun saɓani. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ake magance wannan saɓani.

A lokacin da aka samu rashin jituwa, yana da kyau a yi haƙuri, a kwantar da hankali sannan a tattauna matsalar cikin hikima da mutunta juna. Kowane gida yana da nasa irin ƙalubalen da kuma hanyar da ta dace wajen warware su.

5. A lokacin ƙalubale ne ake gwada ƙarfin aure:

Yawancin lokuta, shekarun farko na aure su ne mafi cike da ƙalubale. A irin wannan lokaci ne ake koyon fahimtar juna, haƙuri da yadda za a warware matsaloli. Abin takaici, wasu ma’aurata kan yi gaggawar yanke hukuncin rabuwa maimakon su nemi mafita. Alhali ƙalubale na iya zama wata hanya ta ƙ

arfafa zaman aure idan aka tunkare su cikin hikima da haƙuri.

6. Haƙuri da juriya su ne ginshiƙan zaman aure:

Haƙuri da juriya suna daga cikin manyan abubuwan da ke tabbatar da zaman lafiya a aure. Duk inda mutane biyu suka haɗu, ba za a rasa bambancin ra’ayi da ɗabi’a ba.

Saboda haka, mace ta kasance mai haƙuri da yafiya, tare da neman mafita cikin natsuwa a duk lokacin da aka samu matsala.

Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa auren magabata ya daɗe yana ɗorewa shine haƙuri, juriya da girmama juna. Waɗannan kyawawan ɗabi’u su ne har yanzu ginshiƙan zaman aure mai albarka.

Aure ba ya ginuwa da soyayya kaɗai. Yana buƙatar ilimi, hawuri, juriya, fahimtar juna da tsoron Allah. Duk macen da ta shirya kanta da waɗannan kyawawan halaye, tana da damar samun zaman aure mai cike da natsuwa, soyayya da albarka.

Allah Ya azurta ƴaƴanmu mata da mazaje nagari, Ya sanya zaman aurensu ya kasance cikin rahama, soyayya da kwanciyar hankali. Amin.

Abubakar Sulaiman
Website |  + posts Bio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

GORON JUMA’A 17-04-2026
Goron Juma'a

Goron Juma’a

June 5, 2026
GORON JUMA’A 01-07-2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 22-05-2026

May 22, 2026
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025
Labarai

Ku Kula Da Kyawawan Ɗabi’u, Su Ne Waɗanda Annabi SAW Ya Kira Duk Halitta A Kansu

April 17, 2026
Next Post
Kofin Duniya

Abubuwa Uku Da Ya Kamata Kusani Akan Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.