ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba

by Bello Hamza
2 months ago
APC

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

Ƙungiyar National Progressiɓes Councillors’ Forum (NPCF), wadda ke wakiltar kansiloli 10,378 na jam’iyyar APC a faɗin Nijeriya, ta yi kira ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya umarci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da na tsaro na tarayya su ɗakatar duk wani bincike ko mataki da ake ɗauka kan koke-koken da ƙungiyar ta bayyana a matsayin marasa tushe kuma masu ɗauke da manufofin siyasa kan Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sakkwato.

A wata sanarwa da aka fitar bayan taron kwata-kwata na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano, NPCF ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yain ɓata suna da hare-haren kafafen yaɗa labarai da ke danganta Sanata Yari da kama ɗanyen zinari na naira biliyan 4.4 a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano a ranar 11 ga watan Yuni. Ƙungiyar ta ce Hukumar EFCC ta bayyana sunayen waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kuma babu sunan Sanata Yari a cikinsu. Haka kuma, ta musanta zarge-zargen da ke cewa yana ɗaukar nauyin zanga-zangar adawa da gwamnati ko kuma tallafa wa jam’iyyar ADC.

Ƙungiyar ta yaba wa irin gudunmawar da Sanata Yari ya bayar a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara da kuma shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya. Ta ce a matsayinsa na mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, babu wata shari’ar cin hanci ko laifi da ke kansa a kotu. NPCF ta kuma ce mulkinsa ya samar da shirin sulhu da afuwa na farko a jihar, gina filin jirgin sama, hanyoyi, cibiyoyin ilimi da kuma jami’ar farko mallakar gwamnatin jihar a Gusau.

ADVERTISEMENT

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta zargi wasu ƴan siyasa daga Arewa maso Yamma da suka kasa samun tikitin takarar gwamna da amfani da muƙaman gwamnati wajen tsoratarwa da matsa lamba ga Sanata Yari. NPCF ta bayyana cewa irin waɗannan matakai na iya kawo cikas ga haɗin kan APC da kuma manufar “Renewed Hope”. Ta kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da sauran masu ikirarin biyayya ga APC su daina abin da ta kira aiki da ke cin karo da muradun jam’iyyar.

APC
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Abin Da Ya Kamata Ka Sani Kan Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

MASU ALAKA

APC
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
APC
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Wang Yi: Sin Da Kasashen Turai Abokan Hadin Gwiwa Ne Ba Na Gaba Ba

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.